Tatsuniyar ’Ya’yan Sarki Da Ƙadangare

0
12

Ga ta nan, ga ta nanku.

Akwai wani Sarki da ’ya’yansa mata su biyu kyawawa. Amma tun suna ƙanana ya hana su fita waje domin tsaron lafiyarsu. Kullum suna gida har suka girma, suka isa aure. Ganin sun kai munzalin aure, sai ya bari suka ɗan fara fita waje.

Ana nan, rannan dai Sarki ya ce zai aurar da su. Manema suka fito. Wannan ya zo, a ce a a, bai yi ba. Wancan ya zo, a hana shi. Wata rana dai sai Sarki ya ce a tara mutane, duk wanda ya kira sunan ɗaya daga cikinsu, to shi za a ba wadda ya faɗi sunanta. Shi
ke nan aka sa ranar tara mutane don a ji wanda zai faɗi sunan.

Matasa da sauran waɗanda ba su wuce auren budurwa ba, kowa ya shiga neman sunayen ’yan matan; abu dai ya gagara. Sai Biri ya sami labari kuma ya ce ya san dabarar da zai yi. Sai ya je ya samo mangwaro nunannu kyawawa guda biyu. Da ya make mangwaron nan biyu, sai ya garzaya cikin lambun Sarki inda yaran suke hira, ya zauna a kan bishiyar da suke zama a gindinta ya shiga jira.

Da suka fito, sai ɗaya daga cikin ’yan matan ta je gindin bishiyar da Biri yake kai, sai ya jefa mangwaro ɗaya. Da ta gani sai ta ɗauka tace: “Kirindi zo ki ga wani nunannen mangwaro na samu.”Wannan ya sa Biri murna saboda ya ji sunan ɗaya daga cikinsu. Da ɗayar ta doshi wajen wadda ta kira ta don ta je ta ga mangwaron Kirindi, sai ya jefa ɗaya mangwaron, sai ita ma ta ganshi.

A cikin murna da ɗoki ta ce: “Ai ni ma na samu Karanda.” Biri na ji sai ya kama murna yana cewa: “Yawwa ai ni zan aure su tun da na ji sunayensu.” Bayan lokacin da Sarki ya yanka wa mutane ya cika, sai aka tara mutane ana tambayar su ko sun sami sunan ’yan matan.

Wannan ya zo ya ce kaza ne, a ce masa a a, wancan ma ya zo bai canka ba. Haka dai aka yi ta fama har aka zo kan malam Biri. Ana zuwa kansa sai aka ji a cikin raɗa saboda tsoro ya ce: “Kirindi da Karanda.” Sai Ƙadangare da ke gefensa ya ji, sai kawai ya yi farat da ƙarfi ya ce: “Kirindi ce da Karanda.”

To shi kuma Sarki ya riga ya yi alkawarin duk wanda ya faɗi sunayensu, zai ba shi su aure. Ba tare da ɓata lokaci ba, aka ba Kadangare auren ’ya’yan Sarki. Ashe Biri ya ji haushin ƙwacen da Ƙadangare ya yi masa, kuma ya saɓi laya sai ya ɗauki fansa a kan Ƙadangare.

Saboda haka bayan an gama bikin amaren Ƙadangare sun tare a gidansa, sai
rannan Biri ya haura dangar gidan gonar Sarki inda Sarki ke kiwo. A cikin dabbobin da Sarki ke kiwo kuwa, akwai wata babbar kazarsa wadda ya fi so a kan duk sauran abubuwan da yake kiwo a gonar.

Sai Biri ya kama wannan kaza ya yanka, ya fige, ya dafa ya cinye. Da ya cinye ya sha ruwa, sai ya kwashe duk gashinta da ƙasusuwanta ya je ya haura dangar gidan Kadangare ya zuba. Gari na wayewa, sai labari ya je ga Sarki cewa an sace masa kaza. Sai ya sa fadawa su bi gida-gida su nemo kazar nan kafin a zahar.

Fadawa na shiga gidan Kadangare, sai suka tarar da gashin kazar Sarki da ƙasusuwa. Suna ganin haka, sai suka kai wa Sarki labari. Saboda kunya da kara irin ta manya, da Sarki ya ji cewa a gidan surukinsa ne aka sami gashi da ƙasusuwan kazarsa, sai ya ce a bar maganar, kuma ya hana a hori Kadangare.

Biri dai bai ji daɗin haka ba. Duk domin ya yi ramuwar gayya, sai ya yanka akuya ya dafa aka yi romo mai kayan yaji. Ya ɗauka ya kai gidan Kadangare, romo da naman akuya suna tafasa saboda zafi. Da Kadangare ya buɗe mazubin, sai ya ga naman akuya da romo, ga ƙamshinsa ya cika gari.

Sai kwaɗayinsa ya tashi, bai yi wata- wata ba sai ya kai bakinsa. Yana ɗosana bakinsa kuwa sai yaƙone, ya ja baya. Matansa na fitowa sai hankalinsu ya tafi kan mazubin nan. Da suka buɗa, suka ga naman akuya ne a cikin romon da ya sha kayan yaji, sai su ma suka kwasa, suna kai wa bakunansu sai zafi ya sa kowacce ta ƙwala ihu, ta tofar da wanda ta guntsa.

Dukkansu uku, watau Kadangare da matansa biyu ba wand abai ƙone ba. Da Biri ya ga haka, sai ya fita daga inda ya maƙe, ya kama hanya ya tafi yana dariyar ƙeta da jin daɗi, ya bar su da jinya. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Kowa ya cuci wani zai ga mummunan sakamako.
  • Duk abin da ka samu ta hanyar rashin gaskiya ba za ka moreshi ta hanyar jin daɗi ba.
  • An ɓata goma ɗaya ba ta gyaru ba.
  • Rabon kwaɗo ba ya hawa sama.

Danna nan don karanta Tatsuniyar Tsurondi

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Tsurondi
Labarin na GabaTatsuniyar Binta ’Yar Sarki
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.