Category: Juna biyu (ciki)

Mun samar da wannan ɓangaren ne domin koyar da ilimin rainon ciki (juna biyu) a cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Za ku iya kai wa gare su ta hanyar amfani da kwamfutoci ko wayoyin hanu.

wikiHausa ta kowa ce. Kowa zai iya taimakawa da ilimi ko gyara. Bugu da ƙari, kowa na iya amfani da wannan kafa domin koya ko koyarwa.

  • Babban Dalilin Da Ke Kawo Rashin Haihuwa [Infertility]

    Babban Dalilin Da Ke Kawo Rashin Haihuwa [Infertility]

    Rashin haihuwa shi ne rashin samun ciki (juna biyu) bayan shafe watanni goma sha biyu “wato shekara guda” ana samun jima’i tsakani ba tare da amfani da wata kariya ba ko maganin hana ɗaukar ciki.

    Sai dai Abin Lura Shi ne

    Rashin haihuwa ba matsalar mace ba ne ita kaɗai, namiji ma matsalar na iya kasancewa daga gare shi, wanda kuma da yawa mazan Kan zargi matan, sai dai akan zargi matsalar daga mace idan matan mutum suka kasance biyu ne kuma ɗayar a ciki ya zamto tana haihuwa to shi ne sai a yi tunanin matsalar daga macen ne.

    Sai dai ba za a iya cewa mutum ba ya haihuwa ba ko da an shafe watanni 12 ,har sai bayan shekara 5 tukun.

    Yana da kyau ku karanta menene Ƙurjin Farji da kuma maganin sa

    Me Ke Jawo Infertility

    A dangane da namiji duk waɗannan abubuwan na iya hana shi haihuwa

    • Ƙarancin ƙwayayen halitta, ko sakamakon haka mutum ya tsinci kansa, ko a sakamakon yawan masturbation, hatsari, da sauransu.
    • Rashin ƙwarin ƙwayayen halitta
    • Cuta me karya garkuwar jiki, ko ciwon asthma.
    • Ciwon sanyi wato fitar farin ruwa daga gaba, musamman masu saduwa da mata barkatai
    • Idan golon mutum suka zamto ƙananu ko ɗaya ya fi ɗaya musamman in suna ciwo
    • Ko wata matsala da ta shafi mazantakarsa wacce ta zamto ta gado ce,kamar ƙanƙantar azzakari ya zamto ba tsayi
    • Cuttuka irinsu ciwon suga.
    A Mata Kuma
    • Ciwon sanyi da ke sa fitar ruwa daga gabansu musamman in an yi sakaci ba tare da neman magani ba, zuwa PID, UTI da cervical cancer.
    • Kumburi a wani sashi na cikin mahaifa wato (polyp)
    • Ƙarin cikin mahaifa (fibroids), mace na iya kaucewa wannan ta hanyar yin aure da wuri, ‘yan mata musamman a yanzu da yawa na haɗuwa da wannan larurar tare da ovarian cyst.
    • Fara sha ko yin allurar magungunan hana ɗaukar ciki kafin haihuwar farko ko kafin fara samun ciki
    • Idan mace ta taɗa samun ciki a wajen mahaifarta (uterus) memakon cikin mahaifa kamar yadda yake.
    • Idan mahaifar mace ta samu matsala ƙila ko sakamakon operation da aka taɓa yi mata a baya.
    • Cuttuka masu wuyar sha’ani kamar asthma ko ciwon suga ga mace.
    • Haihuwarta da wata nakasa wacce ba za ta iya bari ta sami ciki ba (birth defects).

    Wadannan su ne mahimman abubuwan da ka iya hana shigar ciki, sai dai kamar yadda nace ba za a ce gaba ɗaya mace ko namiji ba ya haihuwa ba sai an sami kamar shekara 5 to sannan ne lallai za a fara tunanin haka, sannan a tashi tsaye wajen neman mafita idan matsalar wacce za a iya gyarawa ce.

    Domin karanta bayani akan Fibroid (Karin Mahaifa) Danna nan 

    Alamomin Da ke Nuna Mace Na Iya Fuskantar Wannan Matsala Ta Rashin Haihuwa

    • Rashin ganin jinin al’ada akai-akai kowanne wata sama da kwana 28.
    • Jin zafi tare da ganin jinin al’ada na fita me yawa (heavy bleeding)
    • Rashin al’ada ɗin ma baki ɗaya.
    • Jin zafi yayin saduwa ko yaushe
    • Canzawar sha’awa ta ji ba ma ta so a kusanceta wani lokacin

    Da dai sauransu, don haka wannan matsala ce da sai an dangana ga ƙwararrun likitocin mata, daukar ciki da raino wato (Obstetrics and Gynaecologist) aikinsu ne ba kowanne irin likita ne ke handling wannan case ɗin ba.

    Domin sanin menene Zazzabin Typhoid Danna nan

  • Matakin Kariya Kafin Samun Ciki (Preconceptional care)

    Matakin Kariya Kafin Samun Ciki (Preconceptional care)

    Wannan wasu matakan kariya ne da mace da ta ke da shirin ɗaukar ciki ya kamata ta samu tun kafin samun cikin, domin samun cikarkiyar lafiya lokacin rainon ciki da kuma haihuwa.

    MENE YA SA KIKE BUƘATAR MATAKAN KARIYA KAFIN SAMUN CIKI?

    Tabbatacciyar lafiyar mace kafin samun ciki, yana ɗaya daga cikin manyan mahangar samun lafiyayyen ciki da haihuwa.

    MATAKAN KARIYA.

    1. Ga macen da ta ke da wata cuta da ta ke shan magani a kai, ya kamata likita ya tabbatar mata da cewar cutar ba ta matakin da za ta iya ba ta matsala idan ta samu ciki, wannan cututtuka sun haɗa da:
      -ciwon siga
      -Sikila
      -Asma
      -Ciwon zuciya
      -Hawan jini…… Da sauran su.
      Baya ga haka, akwai wasu maganin da ake sha a waɗannan cututtuka, wanda ka iya ba wa jaririn da za ta haifa matsala, don haka, likita zai canza mata su zuwa ga wanda ba su da matsala a kan jariri.
    2. Folic Acid
      Wannan magani mace kan fara shan sa kafin samun ciki da kuma wata 3 na farkon ciki, bisa shawarar likita. Yana bayar da kariya a kan haihuwar yara masu ƙaramin kai ko buɗaɗɗiyar laka.
    3. Abinci.
      Akwai buƙatar mace ta ƙara samun abincin mai gina ciki da ƙarin lafiya domin ita kanta da kuma jaririn da zai zauna a cikinta.
    4. Barin shan magani barkatai ba tare da shawarar likita ba, saboda akwai magungunan da suke bayar da matsala ga jariri ko su kawo ɓarewar cikin, idan aka samu.

    Danna koren rubutun nan domin karanta Alamomin Shigar Ciki (Juna Biyu) ko yadda ake amfani da na’urar gwajin ciki ko Yadda za ki kare kanki daga Ciwon Kumburi ɓangaren Mahaifar Mace (Pelvic Inflammation Disease (PID))

  • Alamomin Shigar Ciki (Juna Biyu)

    Alamomin Shigar Ciki (Juna Biyu)

    Shin waɗanne alamu ne mace za ta ji ko ta gani idan tana ɗauke da sabon ciki wato juna biyu, ta yadda za ta ga ne tun kafin ta je asibiti a tabbatar.

    Haƙiƙa ba kowace mace ce ta kwan da sanin cewa babban abin da ke kawo ɓatan wata (wato ko juna biyu rashin ganin al’ada ba) shi ne samun juna biyu ba. Musamman a sabbin aure ko kuma a mata marasa kamun kai.

    Bayan juna biyu kuma cuttukan da ke sa shigar ƙwayoyin cuta ciki ko bakin mahaifar mace [uterus] su ne kan gaba wajen kawo ɓatan wata (rashin ganin haila), ko rikicewar lissafin wata.

    SAURAN ABUBUWAN DA KE KAWO ƁATAN WATA SUN HAƊA DA:

    1. Shayarwa
    2. Halin damuwa, ƙunci ko fargaba
    3. Rashin lafiya a yan tsakani.
    4. Bayar da gudunmawar jini
    5. Rashin zama guri guda.
    6. Rashin samun hutu, kamar a masu wasannin motsa jiki ko doguwar tafiyar ƙasa.
    7. Wasu lokuta ma har da shan wasu magunguna barkatai, walau na asibiti ko na gida.

    MENE NE YA KE TABBATAR DA CIKI?

    Ma’ana waɗanne alamu mace mai juna biyu za ta ji ta tabbatar ciki ne? Ga su nan a zayyane:

    A watan farko, mace za ta yi ɓatan wata, bayan ƴan satittuka, sai ta fara samun;

    • Tashin zuciya da sassafe, har da amai a wasu lokutan, koda kuwa ba ta ci komai ba.
    • Saurin gajiya, kasala, ko yaya ta yi wani ɗan aiki.
    • Ko Ganin jiri (dizziness) idan ta zo miƙewa bayan jimawa a zaune.
    • Yawan zubar da miyau, tare da jin sa yana yawan taruwa ga kuma kauri.
    • Zazzaɓi amma ba me zafi can ba, haka dai kurum za ta ji kamar ba ta da lafiya
    • Sai rashin son ƙamshin abu, koda turare ne a wasu lokuta. Tare dajin za6in wani abun daban wanda kafin a jima sai ta ji ta bar sha’awar wannan, ta fara sha’awar wani daban.

    BATUN GWAJIN JUNA BIYUN FA?

    A wane lokaci ne ake so a je a yi gwajin juna biyun in ana kokonton likita ?

    -Akan tabbatar ta hanyar auna fitsari ko jini.

    -Sannan sai ta scanning din hoton ciki, idan ma cikin ne, to ta hanyar hoton za a tabbatar, sannan a tantance shin a cikin mahaifa ya ke, yadda akeso ko wajen mahaifa wato [ectopic pregnancy].

    A watannin da ciki ya fara tsufa kuma wato yakai kamar wata uku (3). Akan ga alamu kamar haka:

    • Girman ciki ya fara bayyana.
    • Yawan jin fitsari ko zaryar yin fitsari, saboda abin da ke ciki ya fara danne marar fitsari.
    • A wasu lokutan akan samu ciwon baya.
    • Ciwon ƙirji wato zafin ƙahon zuci ko kwarnafi saboda ‘acid’ ɗin ciki na tasowa saman ƙirji.
    • Sai kuma a fara samun duhun fuska da fitowar zane a fatar ciki (stretch marks) da buɗewar hanci a wasu da kuma jin nauyi ko ciwon nonuwa.


    Ba dole ba ne kowace mace ta samu dukkan waɗannan alamun, amma fiye da rabin mata suna samun aƙalla rabin waɗannan alamun.

    Allah ka sauki dukkan masu ciki lafiya. Amin

    Danna koren rubutun nan domin karanta yadda ake amfani da na’urar gwajin ciki ko Yadda zaki kare kanki daga Ciwon Kumburi ɓangaren Mahaifar Mace (Pelvic Inflammation Disease (PID))

  • Shin Mai Cikin Da Ta Ajiye Azumi Ciyarwa Za Tayi, Ko Bari Za Tayi Tarama Bayan Ta Haihu?

    Shin Mai Cikin Da Ta Ajiye Azumi Ciyarwa Za Tayi, Ko Bari Za Tayi Tarama Bayan Ta Haihu?

    Amsa: Mai ciki da mai shayarwa, malaman da suka ɗauke su a matsayin marasa lafiya na ɗan lokaci sunce; “Zata rama bayan sallah”.

    Kamar Al-imamu Maalik, malaman da suka ɗaukesu a matsayin marasa lafiya, sunce; “Su ciyar kuma su rama bayan sallah”. Kamar Al-imamu Shafi’i, malaman da suka ɗauke su a matsayin waɗanda baza su iya azumi ba; bisa uzuri na rauni kamar uzurin tsofaffi sunce; “Baza su rama ba, ciyarwa kawai za su yi cikin azumi”

    Kamar Ibnu Abass, Ibnu Umar.

    Hujja: (Fatawar Ibnu Abbas da Ibnu Imar) littafi: Bidaayatul Mujtahid wa Nihaayatul Muqtasid, Ibnu Rushdin.

    Domin karanta cikakken bayani akan Idan Alfijir Ya Fito, Kuma Da Janaba A Jikina Cikin Ramadan, Yaya Azumina? danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Shin Idan Na Kwanta Barci, Sai Na Wayi Gari Janaba Ta Same Ni; Ta Hanyar Mafarki Ko Kwanciyar Aure, Zan Iya Ɗaukar Azumi, Ko Sai Nayi Wanka? danna nan.

    Danna link ɗinnan; https://chat.whatsapp.com/JtD82AjZZmo3AtSTaKP05r domin shiga WhatsApp group namu na Ramadan.

  • Shin Ya Hallata Mai Ciki Ta Ɗauki Azumi?

    Shin Ya Hallata Mai Ciki Ta Ɗauki Azumi?

    Amsa: Shari’ah tace,”Mai ciki ta haƙura da azumi, saboda ƙoshin lafiyar jaririnta”.

    Hujja: “Duk wanda yake cikin halin rashin lafiya, ya rama bayan sallah”.

    Suratul Baqara 184.

    Domin karanta cikakken bayani akan Shin Mai Cikin Da Ta Ajiye Azumi Ciyarwa Za Tayi; Ko Bari Za Tayi Tarama Bayan Ta Haihu?

    Domin karanta cikakken bayani akan Idan Na Ɗauki Yaro Jariri, Sai Yayi Min Tumbuɗi A Cikin Hanci, Yaya Azumina? danna nan.

    Danna link ɗinnan; chat.whatsapp.com/JtD82AjZZmo3AtSTaKP05r domin shiga WhatsApp group namu na Ramadan.

  • Ta Yaya Zan Gina Ƙwaƙwalwar Jaririna Tun Yana Ciki?

    Ta Yaya Zan Gina Ƙwaƙwalwar Jaririna Tun Yana Ciki?

    Za ki iya gina ƙwaƙwalwar jaririnki yana ciki ta hanyar amfani da Folic Acid/Folate.

    Folic acid na ɗaya daga cikin nau’ikan Vitamin B ne (Vitamin B complex), ana samun shi a cikin bushasshen wake, peas, lemon zaƙi, hanta, ganyen salad da dai sauransu.

    Folic acid na taimakawa wajen tattali da kuma ƙyanƙyasar cells, da kuma hana canjin (DNA) wanda yake kaiwa ga cancer. Wannan Folic acid ko kuma folate yana gina ƙwaƙwalwar yaronki a ciki, ƙashin kansa (wanda ya zagaye ƙwaƙwalwar), da kuma lakarsa, domin su hana ginuwar matsaloli kamar neural tube defect; spina bifida.

    Wannan cuta na samar da tawaya a ƙwaƙwalwa da kuma laka, wanda yana faruwa a watan farko na ciki kafin ma mace ta san tana da juna biyu. Misalin hydrocephalus (taruwar ruwa a cikin ƙwaƙwalwa).

    Bugu da ƙari, ba ga jaririnki kaɗai ba, harda kanki ma, rashin folic acid kan haifar da yawan ɓarewar ciki, haifar bakwaini da sauransu.

    Daga ƙarshe nake ba da shawara ga duk wadda take son gina ƙwaƙwalwar jaririnta, da ta ci abubuwan da suke ɗauke da folic acid a ƙalla 400mcg wanda na ambata su a baya.

    Domin karanta cikakken bayani akan Tarbiyar Yaro danna nan

  • Yadda Ake Amfani Da Na’urar Gwajin Ciki (Juna Biyu)

    Yadda Ake Amfani Da Na’urar Gwajin Ciki (Juna Biyu)

    Za a iya gwajin ciki da na’ura a kowane lokaci na rana; amma dai da sassafe shi ne mafi dacewa. (fitsarin farko).

    Ki yi fitsari a cikin roba ko kwano mai tsabta ko kofi ko duk abin da kike ganin fitsari zai iya zama a ciki.

    1. Sai ki yi fitsari a ciki, daidai gwargwado, wanda na’urar ba za ta lume duka a ciki ba
    2. Sai ki saka na’urar a cikin fitsarin; iya wajan tsinin ake so ya taɓa fitsarin.

    Kar ki taɓa wajen nuna sakamakon ko wajan tsinin da hannunki

    1. Sai a tsaida na’urar a tsaye kada fitsarin ya wuce alamar (MAX)
    2. Sai ki bar shi ya ɗan jima a ciki kada ya yi ƙasa da sakon biyar (5)
    3. Bayan ya ɗan jima a ciki, sai ki ciro nau’rar daga cikin fitsarin.
    4. Sai ki sa na’urar ta kalli sama wajan ɓangaran da aka rubuta (MAX).

    Idan ba za ki iya riƙe ta a hannu ba, za ki iya ajiye na’urar a waje mai tsafta domin jiran sakamako, ta yadda wajen alamar rubutun MAX din yana kallon sama.

    Sakamako

    • Idan ki ka ga layi mai launi wanda ya turu sosai guda biyu; to kina da ciki kamar yadda aka nuna a hoton nan.
    • Idan kuma ki ka ga layuka guda biyu masu launi, amma ba turarru ba, kina da ciki.
    • Idan kuma ki kaga layi ɗaya, to ba ki da ciki.
    • Idan kuma ki ka ga layi ɗaya mai launi turarre ɗayan kuma ba turarre ba shi ma ba ki da ciki.

    Karin bayani

    • Yayin da ki ke jiran sakamako, za ki iya lura da layi mai launi yana motsawa a cikin wajen nuna sakamakon, wannan ba matsala.
    • Kina buƙatar jira minti 10 don tabbatar da sakamakon.
    • Ba a amfani da sakamakon da gwajin ya bayar bayan minti 30.
    • Sakamako yakan iya canzawa ya danganta da irin na’urar da ki kai amfani da ita, amma wannan shi ne wanda aka fi amfani da shi.