Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Haba-haba - Tana nufin ba da kulawa ka'in da na'in.
Misali; Ana ta haba-haba da manyan baƙi.
ENG; Taking good care of something (A turance tana nufin haba-haba)
Habaici - Tana nufin magana a fakaice ba tare da ambaton suna ba, amma shi wanda ake da shi ya sani.
Misali; Tun safe take yi wa kishiyarta habaici.
ENG; Indirect Reference (A turance tana nufin habaici)
Hadari - Tana nufin yanayin da ke nuna za a yi ruwan sama.
Misali; Hadari ya taso, da alama za a yi ruwa mai yawa.
ENG; Storm (A turance tan nufin hadari)
Hadda - Tana nufin riƙe abu da ka.
Misali; Usman yana ajin hadda, za su sauke Ƙur'ani cikin shekara ɗaya.
ENG; Memorization (A turance tana nufin hadda)
Haddasa - Tana nufin sila ko zama dalilin faruwar wani abu.
Misali; Zuwanta a makare shi ya haddasa ta rasa gurin zama.
ENG; Cause (A turance tana nufin haddasa)
Haddi - Tana nufin hukuncin da ake wa wanda ya aikata laifi a musulunci.
Misali; Haddin sata yanke hannu ne a musulunci.
ENG; Fixed Punishment for transgressing islamic law (A turance tana nufin haddi)
Hadejia-Jama’are River Basin Development (HJRBD) - Hukumar Haɓaka kogin Haɗeja-jama'are
Hadisi - Tana nufin maganganun manzon Allah SAW.
Misali;Malam Ado yana karanta mana hadisi kullum a makaranta.
ENG: Sayings of prophet Muhammad SAW (A turance tana nufin Hadisi)
Hagu - Tana nufin ɓarin hagu a jikin ɗan Adam, idan aka kalli mutum daga sama zuwa ƙasa, ɓari ɗaya shi ne hagu ɗayan kuma dama.
Misali; Da hannun hagu yake rubutu.
ENG; Left (A turance tana nufin hagu)
Kishiyarta; Dama
Haila - Tana nufin jinin da mata ke fitarwa a kowanne wata.
Misali; Matan da ke haila ba sa shiga masallaci.
ENG; Menstruation (A turance tana nufin haila)