Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ignore - A turance tana nufin biris. Misali; Duk da yana cikin mawuyacin hali amma matarsa ta yi biris da shi saboda rashin kirkinsa. HAU; Biris (Tana nufin nuna halin ko-in-kula da abu ko yin watsi da shi)
Illness - A turance tana nufin cuta. Misali; Wata sabuwar cuta ta ɓullo mai suna korona. HAU; Cuta(Tana nufin rashin lafiya)
Impress - A turance tana nufin burge. Misali; Samarin na ƙoƙarin yin komai don burge 'yan matan su. HAU; Burge (Tana nufin ƙoƙarin janyo ra'ayi ko yardar wani)
Indecent talk - A turance tana nufin batsa. Misali; Wasu daga cikin masu amfani da manhajar TikTok na yawan yin batsa a bidiyoyinsu. HAU; Batsa (Tana nufin zantuttuka na rashin  ɗa'a)
Independent Corrupt Practices Commission (ICPC) - Hukumar Hana Cin Hanci / Hukumar Yaki da Cin Hanci
Independent National Electoral Commission (INEC) - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta Ta Ƙasa
Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria (IPMAN) - Ƙungiyar Dillalan Man Fetur Ta Najeriya
Indigineous Languages Writers Association of Nigeria (ILWAN) - Ƙungiyar Marubuta Ta Harsunan Najeriya
Industrial Training Fund (ITF) - Asusun Horon Ɗalibai na Masana'antu
Information Technology Association OF Nigeria (ITAN) - Ƙungiyar Masana Fasahar Bayanai Ta Najeriya
1 2 3 6