Ƙamus

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ta’adi - Ɓarnatarwa ko tozarta dukiya, kamar kwange ko coge ko wadaka da dukiyar kasa,ko samu da ɓarnar kuɗi ba bisa ka'ida ba.
Ta’ammali - Hulɗa ko kuma yin kowace irin mu'amala da wani abu kamar miyagun kwayoyi, kama daga kan yin kwayoyin da masu siyarwa zuwa kan masu sha.
Taekwondo Federation of Nigeria (TFN) - Hukumar Wasan Taƙwando Ta Najeriya
Talata - Rana ce ta biyu a cikin ranakun mako.  Misali; Ana cin kasuwar duk ranar Talata. ENG; Tuesday (A turance tana nufin rana ta biyu a mako)
Tanyo - Taimakawa gajiyayye ko rarrauna cikin wani al'amari, tallafawa mara karfi ga biyan wata bukata.
Tarkacen Tarihi - Karikice na abubuwan amfani da suke tabbatar da tarihi da wanzuwar wata al'umma a wani wuri.
Tasarrufi - Samarwa da juyawa ko sarrafa abu yadda ya kamata domin amfana da abin.
Taskance - Adana adadin mutane ko ma'aikatun da aka yi wa rijista karkashin wata hukuma.
Taurari - Jam'in tauraro, fitattun mutane musamman 'yankwalisa da 'yanwasa da 'yanfim da sauran mutanen da suka shahara.
Tawaga - Ayari na mutane da suke nufin zuwa wani wuri domin cimma wata manufa ko aiwatar da wani aiki.
1 2 3