Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ɗa - Tana nufin matsayin yaro namiji a gurin iyayensa.
Misali; Audu ɗa ne ga Malam Habu.
ENG; Son (A turance tana nufin ɗa)
Ɗabi’a - Tana nufin hali.
Misali: Yaran gidan suna da kyakkyawar ɗabi'a.
ENG; Behaviour (A turance tana nufin ɗabi'a)
Ɗaci - Tana nufin wani yanayi mara daɗi da ake ji a maƙogwaro idan an ɗanɗana abubuwa kamar magani da sauransu.
Misali; Maganin yana da ɗaci sosai.
ENG; Bitterness (A turance tana nufin ɗaci)
Ɗaukaci - Dukkani, Gabadaya, Kafatani
Ɗauraye - Tana nufin sa ruwa a sake wanke abu.
Misali; Na ɗauraye kwanon kafin in zuba abinci.
ENG; Rinse (A turance tana nufin ɗauraye)
Ɗawafi - Tana nufin zagaye Ka'aba da zimmar ibada.
Misali; Duk wanda ya je Umara sai ya yi ɗawafi.
ENG; Circle the Ka'aba at Macca (A turance tana nufin ɗawafi)
Ɗazu - Tana nufin lokacin da be daɗe da wucewa ba.
Misali; Ɗazu na dawo daga gidan bikin.
ENG; A moment ago (A turance tana nufin ɗazu)
Kishiyarsa; Yanzu
Ɗaɗɗoya - Tana nufin wani ganye mai ƙamshi wanda ake magani da shi.
Misali; An yi amfani da ganyen ɗaɗɗoya wajen haɗa maganin.
ENG; A fragrant herb (A turance tana nufin ɗaɗɗoya)
Ɗigil - Tana nufin ɗan gajere ko ƙanƙani.
Misali; Na ga wani ɗan ɗigil a kasuwa yau.
ENG; Very Short (A turance tana nufin ɗigil)
Ɗimbi - Tana nufin da yawa.
Misali; Muna miƙa godiya mai ɗimbin yawa ga waɗanda suka samu damar zuwa taron buɗe kamfaninmu.
ENG; Superabundance (A turance tana nufin ɗimbi)
1
2