Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Da - Tana nufin tare. Misali; Ni da yayana farare ne. ENG; With (A turance tana nufin da)
Da’ira - Tana nufin zagayayye. Misali; Yara sun yi da'ira suna wasa. ENG; Circle (A turance tana nufin da'ira)
Daddawa - Tana nufin sinadarin girki mai sa ƙamshi da armashin abinci. Misali; Miyar kuka ta fi daɗi idan ta ji daddawa. ENG; Locust bean (A turance tana nufin daddawa)
Dafa - Tana nufin sa abu a cikin tukunya a zuba ruwa a ɗora a wuta har ya yi laushi. Misali; Sai da aka dafa abincin aka yi sadakar da shi. ENG; Cook (A turance tana nufin dafa)
Dafi - Tana nufin abin da ke iya kisa, zai iya kasancewa daga dabbobi ko wani abu daban.  Misali; Dabbobin da suke da dafi suna da hatsari matuƙa. ENG; Poison (A turance tana nufin dafi)
Dafifi - Tana nufin taruwar jama'a da yawa. Misali; Mutane sun yi dafifi a wajen kallon wasan kalankuwa. ENG;Large Mass (A turance tana nufin dafifi)
Daga - Tana nufin gumurzu ko shan fama. Misali; An sha daga da shi kafin ya yadda a yi masa allurar. ENG; Struggle (A turance tana nufin daga)
Dagaci - Tana nufin shugaban ƙauye. Misali; An naɗa shi dagaci a ƙauyensu. ENG; Village Head (A turance tana nufin dagaci)
Dagargaza - Tana nufin farfasa abu a yi masa rugu-rugu. Misali; Matasan sun dagargaza gilasan ginin yayin faɗace-faɗacensu. ENG; Crush (A turance tana nufin dagargaza)
Dage - Tana nufin yin ƙoƙari matuƙa. Misali; Ya dage da karatu har sai da ya ci jarrabawarsa. ENG; Strive (A turance tana nufin dage)
1 2 3 12