Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Fa’ida - Tana nufin amfanin abu.
Misali; Zumunci yana da fa'ida don yana sa albarka a rayuwa.
ENG; Usefulness (A turance tana nufin fa'ida)
Kishiyarta; Rashin Fa'ida
Fabrairu - Wata ne na biyu a shekara.
Misali; Za a gudanar da taron a watan Fabrairun wannan shekarar.
ENG; February(A turance yana nufin wata na biyu a shekara)
Facaka - Tana nufin kashe kuɗi ba tare da la'akari ba.
Misali; Tun da aka raba musu gado yake facaka da kuɗi.
ENG; Squandering (A turance tana nufin facaka)
Face - Tana nufin sai dai.
Misali; Babu wanda zai makara face ya kasance mai saɓa alƙawari.
ENG; Except (A turance tana nufin face)
Face - A turance tana nufin fuska.
Misali; Ta mare shi a fuska hakan ya janyo suka fara faɗa.
HAU; Fuska (Tana nufin sashen jiki mai ƙunshe da ido da hanci da baki)
Faci - Tana nufin sacewar taya.
Misali; Tayar keken ta yi faci sai an an gyaro.
ENG; Patch (A turance tana nufin faci)
Facial Markings - A turance tana nufin jarfa.
Misali; Jarfa, gadon gidansu ne.
HAU; Jarfa (Tana nufin tsagun fuska)
Faffaɗar Jami’ar Najeriya - National Open University Of Nigeria (NOUN)
Fage - Tana nufin fili ko dandali.
Misali; An ba wa 'yan dambe fage don su fafata.
ENG; Open Space/Arena (A turance tana nufin fage)
Fahimta - Tana nufin ganewa.
Misali; Ɗaliban suna da fahimta ƙwarai da gaske.
ENG; Understand (A turance tana nufin fahimta)
Kishiyarta; Rashin Fahimta