Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Obedience - A turance tana nufin biyayya. Misali; Aisha tana da biyayya. HAU; Biyayya (Tana nufin yin abinda aka ce a yi da barin abinda aka hana)
Obligatory - A turance tana nufin farilla. Misali; Yin salla sau biyar a kowacce rana farilla ne akan kowane musulmi. HAU; Farilla (Tana nufin dole)
October - A turance yana nufin wata na goma a shekara. Misali; Najeriya ta samu 'yanci a ranar ɗaya ga watan Oktoba 1960. HAU; Oktoba (Wata ne na goma a shekara)
Office of the Accountant-General of the Federation - Ofishin Babban Akawun Gwamnatin Tarayya
Office of the Head of Civil Service of the Federation - Ofishin Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya
Office of the National Security Adviser - Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa Kan Tsaro
Office of the Surveyor-General of the Federation - Ofishin Shugaban Safiyo Na Gwamnatin Tarayya
Oil Mineral Producing Areas Development Commission (OMPADEC) - Hukumar Raya Yankuna Masu Arzikin Man Fetur
Oktoba - Wata ne na goma a shekara. Misali; Najeriya ta samu 'yanci a ranar ɗaya ga watan Oktoba 1960. ENG; October (A turance yana nufin wata na goma a shekara)
On top/above - A turance tana nufin bisa. Misali; Littattafan na bisa teburi. Kishiyarta; Ƙarƙashin HAU; Bisa (Tana nufin a kan wani abu)
1 2 3