Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

safiyo - Awo ne na zubin kasar da za a gina a matsayin gari ko mahalli.
Salary/Wage - A turance yana nufin albashi. Misali; An biya ma'akata albashi yau da safe. HAU; Albashi (Yana nufin kuɗi da ake biyan mutum sakamakon aikin da ya yi a wata ko sati)
Sallah - Sallah wata nau'in ibace da mutane musulmai suke gabatar da ita a matsayin bauta ga Allah da yayi halitta. Jam'i ; Salloli
Satumba - Wata ne na tara a shekara.  Misali; Sabon zangon karatuna farawa ne a watan Satumba. ENG; September (A turance yana nufin wata na tara a shekara)  
Saturday - A turance tana nufin rana ta shida a mako.  Misali; Ranar Asabar ne bikin. HAU; Asabar (Rana ce ta shida a ranakun mako)
Scheme - Shiri, Tsari
Science Teachers Association of Nigeria (STAN) - Ƙungiyar Malaman Kimiyya Ta Najeriya
Search - A turance yana nufin biɗa. Misali; Ya samu abinda ya je biɗa a balaguron da ya yi. HAU; Biɗa (Tana nufin nema ko lalube)
Search - A turance tana nufin caje. Misali; Na caje yaran duka ban ga wanda ya ɗauki littafin ba. HAU; Caje (Tana nufin duba ko ina)
Second (of time) - A turance tana nufin daƙiƙa. Misali; Na samu faɗuwar gaba na tsawon daƙiƙa ashirin saboda firgicin da na shiga. HAU; Daƙiƙa (Tana nufin motsawar da ƙaramin hannun agogo yake yi)
1 2 3 8