Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ja - Tana nufin launin ja.
Misali; Akwai launin ja a jikin kayan da ya saka.
ENG; Red (A turance tana nufin ja)
Ja - Tana nufin janyowa.
Misali; Ya ja igiyar da ƙarfi shi yasa ta tsinke.
ENG; Pull/Drag (A turance tana nufin ja)
Ja’iba - Tana nufin masifa ko rashin sa'a ko ibtila'i.
Misali; Ya ga ja'iba, bayan ya rasa ɗansa shagonsa ya kama da wuta.
ENG; Misfortune/Calamity (A turance tana nufin ja'iba)
Ja’iri - Tana nufin mara kunya.
Misali; Babu mai yin rawar Gala sai ja'iri.
ENG; Shameless/Disrespectful Person (A turance tana nufin ja'iri)
Ja-gaba - Tana nufin shugaba ko jagora.
Misali; Annabi SAW shi ne ja-gaban dukkan halitta.
ENG; Leader/Guide (A turance tana nufin ja-gaba)
Jabu - Tana nufin abin da ba shi da inganci.
Misali; Madarar jabu ce, idan aka sha tana sa ciwon ciki.
ENG; Fake (A turance tana nufin jabu)
Jackal - A turance tana nufin dila.
Misali; Akwai dila a cikin dabbobin da na gani a gidan ajiye namun daji.
HAU; Dila (Tana nufin wata dabba mai kama da akuya amma ta fi akuya siranta)
Jaddada - Tana nufin tabbatarwa.
Misali; Shugaban makarantarmu ya jaddada mana muhimmancin taron iyayen yara da za a yi gobe.
ENG; Reform (A turance tana nufin jaddada)
Jagab - Tana nufin tsananin jiƙewa.
Misali; Ruwa ya jiƙa su jagab saboda ba su daɗe da fita ba ya sakko.
ENG; Very Wet (A turance tana nufin jagab)
Jahili - Tana nufin wanda ba shi da ilimi.
Misali; Rashin zuwa makaranta ne ke mai da mutum jahili.
ENG; Illiterate Person (A turance tana nufin jahili)