Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Cabbage - A turance tana nufin kabeji.
Misali; A cikin dambun akwai wadataccen kabeji.
HAU; Kabeji (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan lambu wanda ake sarrrafa shi ta hanyoyi daban-daban)
Caca - Tana nufin wasan kati ne da ake sa kuɗi ko wani abu da zimmar wanda ya yi nasara ya ci wannan kuɗin ko abinda aka sa.
Misali; A hanyar akwai dandalin da 'yan caca suke zama.
ENG; Gambling (A turance tana nufin caca)
Cafe - Tana nufin kama abu da sauri.
Misali; Mai tsaron ragar ya cafe ƙwallon da aka bugo masa.
ENG; Catch Something (A turance tana nufin cafe)
Caftan - A turance tana nufin kaftani.
Misali; Yayin kaftani ake yi yanzu.
HAU; Kaftani (Tana nufin taguwa mai faffaɗan hannu)
Caje - Tana nufin duba ko ina.
Misali; Na caje yaran duka ban ga wanda ya ɗauki littafin ba.
ENG; Search (A turance tana nufin caje)
Cak - Tana nufin tsayawa ba tare da motsi ba.
Misali; Sojojin sun tsaya cak har tsawon awa ɗaya.
ENG; Stock still (A turance tana nufin Cak)
Caka - Tana nufin soka abu da ƙarfi.
Misali; Mahaucin ya caka wuƙa a jikin naman ragon.
ENG; Stab (A turance tana nufin caka)
Cakulkuli - Tana nufin taɓa kwuiɓin mutum da zimmar sa shi dariya.
Misali; Sadiya tana yi wa ƙaninita cakulkuli yana dariya.
ENG: Tickling (A turance tana nufin cakulkuli)
Cakuɗa - Tana nufin a yi ta jujjuya abu.
Misali; Amina tana cakuɗa kwaɗon zogale.
ENG; Mix Thoroughly (A turance tana nufin cakuɗa)
Cakwaikwaiwa - Tana nufin tsuntsuwa ma'abociyar rera waƙa.
Misali; Na ji cakwaikwaiwa na waƙa a kan bishiya a makarantar mu.
ENG; Sterling (A turance tana nufin cakwaikwaiwa)