Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Lack - A turance tana nufin fatara.
Misali; Gidan suna fatarar abinci.
HAU; Fatara (Tana nufin rashin kuɗi ko abin duniya)
Lahadi - Rana ce ta ƙarshe a mako.
Misali; A kan ɗaura aure a ranar Lahadi.
ENG; Sunday (A turance tana nufin Lahadi, rana ta ƙarshe a mako)
Lake Chad Research Institute (LCRI) - Cibiyar Binciken Tafkin Cadi
Land-monitor - A turance tana nufin damo.
Misali; Ana masa kirari da damo sarkin haƙuri.
HAU; Damo (Tana nufin dabba mai siffar ƙadangare amma ta fi ƙadangare girma)
Laraba - Rana ce ta uku a cikin ranakun mako.
Misali; Ranar Laraba za a fara jarabawar.
ENG; Wednesday (A turance tana nufin rana ta uku a mako)
Large - A turance tana nufin danƙwalele.
Misali;Na siyowa kakata danƙwalelen goro a kasuwa.
HAU;Danƙwalele (Tana nufin babba ko mai girma)
Large hen - A turance tana nufin daƙwalwa.
Misali; Kazar daƙwalwa ce don ta ƙosar da mu.
HAU; Daƙwalwa (Tana nufin babbar kaza ma'abociyar tsoka)
Large hoe with wide blade - A turance tana nufin garma.
Misali; Gatari ba zai yi aikin nan ba sai dai a sa garma.
HAU; Garma (Tana nufin ƙaton gatari mai faffaɗan kai)
Large Mass - A turance tana nufin dafifi.
Misali; Mutane sun yi dafifi a wajen kallon wasan kalankuwa.
HAU; Dafifi (Tana nufin taruwar jama'a da yawa)
Large needle - A turance tana nufin basilla.
Misali; Na yi amfani da basilla na ɗinke buhun kayana.
HAU; Basilla (Tana nufin allura babba da ake amfani da ita wajen ɗinke buhu ko ƙwarya da sauransu)