Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Radio, Television & Theatre Workers Union (RATTAWU) - Ƙungiyar Ma'aikatan Gidan Radiyo da Talabijin da Wasannin Daɓe
Rain-Cloud - A turance tana nufin girgije.
Misali; Girgije ya lulluɓe sararin samaniya.
HAU; Gajimare (Tana nufin gajimaren da yake ɗauke da ruwa)
Rainy Season - A turance tana nufin damina.
Misali; Lokacin damina ni'ima na sauka kuma ana samun iska sassanya.
HAU; Damina (Tana nufin lokacin ruwan sama)
Raised Doorstep - A turance tana nufin dandali.
Misali; Inna tana zaune a kan dandamali.
HAU; Dandamali (Tana nufin ɗan tudu da ake yi kofar ɗaki)
Rape - A turance tana nufin fyaɗe.
Misali; Ƙungiyar tana yaƙi da masu fyaɗe a jihar baki ɗaya.
HAU; Fyaɗe (Tana nufin yin tarayya da mace ta ƙarfi ba da son ranta ba)
Raw Materials Research & Development Council (RMRDC) - Hukumar Bunƙasa Binciken Ɗanyen Kaya
Reach Limit - A turance tana nufin intaha.
Misali; Darasin ya zo intaha, sai mun haɗu wani lokaci sai mu ɗora.
HAU; Intaha (Tana nufin ƙarshe)
Real Estate Developers Association of Nigeria (REDAN) - Ƙungiyar Masu Sana'ar Gina Mahalli Ta Najeriya
Reap - A turance tana nufin girbi.
Misali; Manoman na cikin farin ciki sakamakon lokacin girbi ya yi.
HAU; Girbi (Tana nufin kwashe amfanin gona bayan ya gama nuna)
Reason - A turance tana nufin hujja.
Misali; Sun yi rashin nasara saboda ba su da ƙwaƙƙwarar hujja a shari'ar.
HAU; Hujja (Tana nufin dalili)