Ƙamus

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ma’adinai - Albarkar ko arzikin da ake samu ko hakowa daga karkashin kasa kamar zinare (gwal) ko tama ko azurfa ko mai da makamantansu.
Mabada - masu ba wa mutane musamman dalibai a makarantu shawarwari game da rayuwa da  kuma cigaban karatunsu.
Mabambanta - Abubuwa masu bambanci da juna ta wasu fuskoki na musamman.
Mahuldanta - Mutane masu kwarewa wajen kai-komo a tsakani ko iya saurarar koken abokan hulda a ma'aikatu da masana'antu.
Majibanta - Masu taimakawa jama'a
Makamashi - Sinadarin da ake hada wuta ko makami da shi kamar itace ko uraniyam.
Makaranta - Makaranta wuri na koyon ilimi wanda mutane suke zuwa dan koyon karatu,kamar yara ko manya jinsin maza da mata suke zuwa dan koyon ilimin addini ko na boko.
makaraya - Masu kai ƙara kotun shari'a, waɗanda suke shari da wani/wasu a gaban Alƙali.
Makimanta - Masu kimanta darajar ƙasa ko gida, musamman wajen kimanta darajar muhalli.
manufacturers Association of Nigeria (MAN) - Ƙungiyar Kamfanonin Ƙere-Ƙere-Ta Najeriya
1 2 3 4