Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Dagi - Tana nufin tafin ƙafar dabbobi masu ƙafa huɗu kamar kare da mage da sauransu.
Misali; Na ga shatin dagi a ƙofar gida, amma ya fi kama da na kare.
ENG; Paw (A turance tana nufin dagi)
Dago-dago - Tana nufin ragowar abinci.
Misali; Akwai dago-dago a ɗakin girki, a ba wa almajirai idan sun yi bara.
ENG: Left-over Food (A turance tana nufin dago-dago)
Dagula - Tana nufin lalatawa.
Misali; Yaran aji ɗaya sun dagula littattafansu.
ENG; Spoil (A turance tana nufin dagula)
Dai-dai - Tana nufin yadda ya dace.
Misali; Wanda ya yi aikinsa dai-dai zai samu sakamako da kyautatawa.
ENG; Correctly (A turance tana nufin dai-dai)
Dai-dai - Tana nufin yadda ya dace.
Misali; Wanda ya yi aikinsa dai-dai zai samu sakamako da kyautatawa.
ENG; Correctly (A turance tana nufin dai-dai)
Daji - Tana nufin gurin da babu mutane sai bishiyu da ciyayi.
Misali; Mafarauta na shiga daji don kamo namun daji.
ENG; Bush (A turance tana nufin daji)
Dakali - Tana nufin gini mai ɗan tudu da ake yi a ƙofar gida don zama.
Misali; Baba yana zaune a kan dakali da abokinsa suna hira.
ENG; Low mud platform outside compound (A turance tana nufin dakali)
Dakaru - Jam'in dakare, jarumai masu tafiya yaki a kafa, kamar sojan kasa a yanzu.
Dakau - Tana nufin yin daka a matsayin sana'a.
Misali; Matar Ado dakau take yi a unguwarsu.
ENG: Pounding corn for pay (A turance tana nufin dakau)
Dakile - Hanawa, kamar hana wani al'amari musamman mara kyau ko barna cigaba da faruwa ko yaduwa