Ƙamus

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

All Local Governments Of Nigeria (AlGON) - Ƙungiyar ƙananan Hukumomi Ta Najeriya
Allo - Abin rubutu ne galibi na katako. Misali; Malami yana rubutu a kan allo. ENG; Blackboard (A turance yana nufin allon rubutu)
Almajiri - Yaro ne da yake koyon karatun addini. Misali; Abbas almajiri ne. ENG; Pupil/Student (A turance yana nufin Dalibin Ƙur'ani)
Alqalami - Alƙalami:abin da ake rubutu da shi. Jam'i : Alƙalama.
Amalgamated Union Of Public Corporations, Civil Service Technical Recreational Services Employees (AUPCTRSE) - Gamayyar ƙungiyoyin ma'aikatan masana'antu da kamfanonin Gwamnti da wuraren shakatawa Ta ƙasa
Amarya - Tana nufin macen da aka ɗaurawa aure. Misali; Lami amarya ce. ENG; Bride (A turance tana nufin amarya)
Ambaliya - Tana nufin ɓarkewar ruwa daga inda yake a tsare ko kuma yawaitar ruwan sama har ta kai ga ya yi ɓarna. Misali; An yi ambaliyar ruwa a jihar Borno a shekarar 2024. ENG; Flood (A turance tana nufin ambaliya)
Ambulan - Tana nufin motar ɗaukan mara lafiya zuwa asibiti.  Misali; An ɗauki waɗanda suka yi hatsarin a ambulan za a kai su babban asibiti. ENG; Ambulance (A turance tana nufin motar ɗaukan mara lafiya)
Ambulance - A turance tana nufin motar ɗaukan mara lafiya.  Misali; An ɗauki waɗanda suka yi hatsarin a ambulan za a kai su babban asibiti. HAU; Ambulan (Tana nufin motar ɗaukan mara lafiya zuwa asibiti)
Amnestic Psychology Association (APA) - Ƙungiyar masana mutuntaka Ta Amurka
1 4 5 6 7 8 11