Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Gaɓar Teku - Iyaka ko fadin inda kasa, kamar najeriya take iko da shi a cikin teku.
Ghost - A turance tana nufin fatalwa.
Misali; An ce fatalwar Idi tana fitowa da daddare.
HAU; Fatalwa (Tana nufin wanda ya mutu ya dinga gizo)
Giant Male Rat - A turance tana nufin burgu.
Misali; Da zan je makaranta na ga wani burgu ya shige rami da gudu.
HAU; Burgu (Tana nufin jibgegen namijin ɓera)
Gidan Rediyon Caina/Sin - China Radio International (CRI)
Gidan Rediyon Faransa - Radio France International (RFI)
Gidauniyar Cinikayya Ta Najeriya da Amurka - Nigerian American Chamber of Commerce (NACC)
Gidauniyar Haɗin Guiwar Bunƙasa Sabuwar Afirka - New Partnership for Africa's Development (NEPAD)
Gidauniyar Kyautata Tattalin Arziki da Zumunta - Socio-Economic Rights & Accountability Project (SERAP)
Gift from God - A turance tana nufin baiwa.
Misali; Yaran aji ɗaya suna da baiwa ta musamman, don suna saurin gane karatu.
HAU; Baiwa (Tana nufin wani abu na musamman da Allah yake ba wa bayinsa wanda ya bambanta su da sauran mutane)
Ginger - A turance tana nufin citta.
Misali; An zuba wadatacciyar citta a yajin.
HAU; Citta (Tana nufin ɗaya daga cikin sinadaran abinci mai inganci ga lafiya, tana da yaji, kuma akwai ɗanya akwai busasshiya)