Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Fat - A turance tana nufin ɓulele.
Misali; Sabon ɗalibin da aka kawo mana ɓulele ne.
HAU; Ɓulele (Tana nufin mai ƙiba)
Fata - Tana nufin abin da ya lulluɓe jikin mutum ko dabba.
Misali; Ana amfani da fata don yin jakunkuna da takalma.
ENG; Skin (A turance tana nufin fata)
Fatali - Tana nufin watsi da abu.
Misali; Alƙali ya yi fatali da hujjojin da aka bayar.
ENG; Disregard (A turance tana nufin fatali)
Fatalwa - Tana nufin wanda ya mutu ya dinga gizo.
Misali; An ce fatalwar Idi tana fitowa da daddare.
ENG; Ghost (A turance tana nufin fatalwa)
Fatara - Tana nufin rashin kuɗi ko abin duniya.
Misali; Gidan suna fatarar abinci.
ENG; Lack (A turance tana nufin fatara)
Fatari - Tana nufin siket ɗin da mata suke sa wa a ƙasan kaya.
Misali; Ta shanya fatari a igiya bayan ta wanke.
ENG; Woman's Underskirt (A turance tana nufin fatari)
Fatauci - Tana nufin tafiya daga wani gari zuwa wani gari don siye da siyar da kaya.
Misali; Idi ya tafi fatauci wata biyu da suka wuce.
ENG; Trading (A turance tana nufin fatauci)
Father - A turance tana nufin mahaifi.
Misali; Baba yana da jikoki arba'in a yanzu.
HAU; Baba (Tana nufin mahaifi)
Fatsa - Tana nufin abin kama kifi.
Misali; Ya ɗauki fatsa ya nufi kogi zai yi su.
ENG; Fish-hook (A turance tana nufin fatsa)
Fawa - Tana nufin sana'ar siyar da nama.
Misali; Wanda zai aure ta fawa yake.
ENG; Butchering (A turance tana nufin fawa)