Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Carkwai - Tana nufin zaƙi sosai.
Misali; Raken yana da zaƙi carkwai.
ENG; Very Sweet (A turance tana nufin carkwai)
Carrying load for payment - A turance tana nufin dako.
Misali; Ƙungiyar masu dako sun koka kan ƙarancin biyansu da mutane ke yi.
HAU; Dako (Tana nufin ɗaukarwa mutum kaya a kai masa inda yake so, ya biya)
Casa - Tana nufin cire tsaba daga cikin kwansonta, kamar shinkafa da gero da sauransu.
Misali; Sai an casa shinkafar sannan za a dafa.
ENG; Thresh Grain (A turance tana nufin casa)
Catch Something - A turance tana nufin cafe.
Misali; Mai tsaron ragar ya cafe ƙwallon da aka bugo masa.
HAU; Cafe (Tana nufin kama abu da sauri)
Caɓa - Tana nufin yin ado da yawa.
Misali; Amaryar ta caɓa ado sosai.
ENG; Make Slushy (A turance tana nufin caɓa)
Caɓi - Tana nufin jiƙaƙƙiyar ƙasa.
Misali; Ka yi hankali da caɓi a hanyar saboda jiya an kwana ana ruwa.
ENG; Mud (A turance tana nufin caɓi)
Celebration - A turance tana nufin biki.
Misali; Zan je biki gobe da yamma, ƙanwata ce za ta yi aure.
HAU; Biki (Tana nufin tara mutane su ci su sha saboda taya murnar wani abin farin ciki da ya samu)
Cement Block - A turance tana nufin bulo.
Misali; Gidan da aka gina da bulon siminti ya fi ƙarko.
HAU; Bulo (Tana nufin abin da ake amfani da shi don yin gini)
Central Bank Of Nigeria (CBN) - Babban bankin najeriya/Babban Bankin kasa
Central Intelligence Agency (CLA) - hukumar leƙen Asiri (ta ƙasar Amurka)