Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Day before festival day - A turance tana nufin jajibere. Misali; Yau jajiberen ƙaramar sallah. HAU; Jajibere (Tana nufin kwana ɗaya kafin ranar biki (sallah ko wani shagali))
Day Of Resurrection - A turance tana nufin kiyama. Misali; Allah SWT shi ya san ranar da kiyama za ta tashi. HAU; Kiyama (Tana nufin ranar tsayuwa, wato ranar da za a tashi ababen halitta a yi musu hisabi)
Daɗe - Tana nufin ɗaukan lokaci mai tsaho. Misali; Yau ɗaliban sun daɗe ba a tashe su ba. ENG; Last Long (A turance tana nufin daɗe)
Daƙiƙa - Tana nufin motsawar da ƙaramin hannun agogo yake yi. Misali; Na samu faɗuwar gaba na tsawon daƙiƙa ashirin saboda firgicin da na shiga. ENG; Second (of time) (A turance tana nufin daƙiƙa)
Daƙiƙi - Tana nufin wanda ba ya gane karatu. Misali; Sun ce masa daƙiƙi saboda ya faɗi jarrabawa. ENG; Dull (A turance tana nufin daƙiƙi)
Daƙuwa - Tana nufin alawar da ake yin ta da niƙaƙƙiyar gyaɗa da aya da sikari. Misali; Zan kai wa amarya daƙuwa saboda idan ta yi baƙi ta ba su. ENG; Sweet made from ground tigernuts and groundnut (A turance tana nufin daƙuwa)
Daƙwalwa - Tana nufin babbar kaza ma'abociyar tsoka. Misali; Kazar daƙwalwa ce don ta ƙosar da mu. ENG; Large hen (A turance tana nufin daƙwalwa)
Deaf person - A turance tana nufin kurma. Misali; Tun yana yaro ya zama kurma sakamakon ciwon baƙon dauro da ya yi. HAU: Kurma (Tana nufin mai ɗauke da lalurar rashin ji)
Death (of prophets or saints) - A turance tana nufin faku. Misali; Ba su san annabi ya faku ba. HAU; Faku (Tana nufin mutuwar annabawa ko bayin Allah salihai)
Debt - A turance tana nufin bashi. Misali; A bashi ya karɓo kayan gininsa. HAU; Bashi (Tana nufin karɓar kuɗi ko wani abu da zimmar biya daga baya)
1 85 86 87 88 89 337