Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Dankali - Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in abinci. Misali; Ina son dankali musamman soyayye. ENG; Potatoes (A turance tana nufin dankali)
Danna - Tana nufin amfani da hannu a ba da ƙarfi akan abu. Misali; Ina ta danna ƙofar amma ta ƙi buɗuwa. ENG; Press (A turance tana nufin danna)
Danshi - Tana nufin lema ko ruwa kaɗan da ke haddasa sanyi a guri ko jikin wani abu. Misali; Kayan suna da danshi, ba su ƙarasa bushewa ba. ENG; Dampness (A turance tana nufin danshi)
Danƙa - Tana nufin kamo mutum da hannu. Misali; Ya sha danƙa a gurin 'yan sanda kuma jikinsa zai gaya masa. ENG; Grasp With Hand (A turance tana nufin danƙa)
Danƙo - Tana nufin abu mai mannewa. Misali; Hannayensa danƙo suke saboda ya sha alawa. ENG; Gum (A turance tana nufin danƙo)
Danƙwalele - Tana nufin babba ko mai girma. Misali;Na siyowa kakata danƙwalelen goro a kasuwa. ENG;Large (A turance tana nufin danƙwalele)
Dara - Tana nufin wasa da ake yi a kan katako mai faɗi, yana kama da wasan ludo. Misali; Da yamma ake wasan dara a majalisar. ENG; Game like draughts (A turance tana nufin dara)
Daraja - Tana nufin muhimmanci ko tsada. Misali; Zinare na da daraja a halin yanzu. ENG; Worth, Value (A turance tana nufin daraja)
Darasi - Tana nufin abin da za a koya. Misali; Malamin na koyar da darasin Lissafi. ENG; Lesson (A turance tana nufin darasi)
Dare - Tana nufin lokacin duhu bayan faɗuwar rana. Misali;Idan dare ya yi iska mai sanyi tana sakkowa. ENG; Night (A turance tana nufin dare)
1 83 84 85 86 87 337