Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ƙoƙuwa - Tana nufin saman hula. Misali: An ƙawata ƙoƙuwar hular da zare mai launi. ENG: Top of Cap (A turance tana nufin ƙoƙuwa)
Ƙubaka - Tana nufin wajen saka tazuge da ke saman wando. Misali: Telan ya gyara ƙubakar wandon domin igiyar ta shiga sosai. ENG: Hem for trouser string (A turance tana nufin ƙubaka)
Ƙuda - Tana nufin ƙaramin ƙwaro mai tashi wanda ake yawan samu a kusa da abinci ko ƙazanta. Misali: Ƙuda na yawan taruwa a kan abincin da aka bari a buɗe. ENG: Fly (A turance tana nufin ƙuda)
Ƙudundune - Tana nufin kwanciya a nannaɗe ko a dunƙule saboda jin sanyi, ko ciwo. Misali: Yaron ya ƙudundune a kan tabarma saboda yana jin sanyi. ENG: Lie curled up (A turance tana nufin ƙudundune)
Ƙudura - Tana nufin yanke shawara da cimma matsayar yin wani abu bayan an yi tunani. Misali: Ya ƙudura a ransa cewa zai ci gaba da karatunsa duk da tarin ƙalubalen da yake fuskanta. ENG: Decide (A turance tana nufin ƙudura)
Ƙufula - Tana nufin saurin fushi. Misali; Ƙufula ya yi har ta kai ga ya mare shi. ENG; Quick-Tempered (A turance tana nufin ƙufula)
Ƙugi - Tana nufin ƙara. Misali: Ana jin ƙugin cikinsa saboda ciwon da yake masa. ENG: Groaning (A turance tana nufin ƙugi)
Ƙugiya - Tana nufin lanƙwasasshen ƙarfen da ake amfani da shi wajen rataya, kama abu, ko jawo wani abu. Misali: Ya rataye rigarsa a ƙugiyar da ke jikin bango. ENG: Hook (A turance tana nufin ƙugiya)
Ƙwadago - Dukkan wani irin aikin da mutum zai yi a biya shi kudi a matsayin lada ko albashi.
Ƙwaƙƙwafi - Bin diddigi domin gano wani ɓoyayyen al'amari.
1 335 336 337