Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
A large edible toad - A turance tana nufin bududdugi.
Misali; Matasan na gasa bududdugi a dandali.
HAU; Bududdugi (Tana nufin ƙaton kwaɗo wanda ake iya ci)
A less favoured wife - A turance tana nufin bora.
Misali; Lami bora ce a gidan Alhaji Mato.
HAU; Bora (Tana nufin matar da ba ta da cikakken gata a gurin mijinta)
Abarba - Abarba na ɗaya daga cikin kayan marmari mai zaƙi, tana da amfani sosai a jikin ɗan adam.
Jam'i : Abarba
Abinci - Yana nufin duk abinda za a ci ya kawar da yunwa.
Misali; Muna cin abinci sau uku a rana.
ENG; Food/Meal (A turance yana nufin abinci)
Abuja Geographic Information System (AGIS) - Hukumar Tsara mahalli Ta Abuja
Abundantly - A turance tana nufin birjik.
Misali; Kaya ne birjik a shagon su Bala, sai wanda ka zaɓa.
HAU; Birjik (Tana nufin da yawa ko adadi mai yawa)
Academic Staff Union Of Polytechnics (ASUP) - Ƙungiyar malaman manyan makarantun fasaha
Academic Staff Union Of Secondary Schools (ASUSS) - Ƙungiyar Malaman Makarantun Sakandare
Academic Staff Union of Universities (ASUU) - Kungiyar Malaman Jami'a
Academy - Makaranta, Cibiya