Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Wages - A turance tana nufin jinga. Misali; Mun yi jinga da shi zai biya ni da zarar na kammala aikin. HAU; Jinga (Tana nufin yarjejeniyar biyan kuɗi)
Waistcoat - A turance tana nufin falmaran. Misali; Falmaran ɗin da yarima ya sa ta yi kyau ƙwarai da gaske. HAU; Falmaran (Tana nufin riga mara hannu da ake ɗorawa a kan mai dogon hannu)
Wake up - A turance tana nufin Farka. Misali; Jaririn ya farka tun ɗazu. HAU; Farka (Tana nufin tashi daga bacci)
Wall - A turance tana nufin garu. Misali; Ƙadangare yana yawo a juikin garu. HAU; Garu (Tana nufin bango)
Warning - A turance yana nufin gargaɗi. Misali; Shugaban ɗalibai ya yi wa ɗalibai gargaɗi akan zuwa makaranta a makare. HAU; Gargaɗi (Tana nufin jan kunne ko yin hani)
Watch - A turance tana nufin kallo. Misali; Yana shigowa ɗakin taron kowa ya bi shi da kallo. HAU; Kallo (Tana nufin duba izuwa wani abu)
Water from leaky roof - A turance tana nufin bi-bango. Misali; Ɗakin ruwa yana bi-bango musamman idan ana ruwa da yawa. HAU; Bi-bango (Tana nufin ruwa ya dinga biyo bango daga rufin kwano)  
Watermelon - A turance tana nufin kankana. Misali; Kankana ta fi yawa a cikin kayan marmarin da muka siyo. HAU; Kankana (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan maramari mai ɗauke da ruwa sosai a ciki)
Wealth - A turance tana nufin daula. Misali; Lami tana cikin daula saboda mijinta yana da kuɗi. HAU; Daula (Tana nufin dukiya ko kayan alatu da ƙawa na duniya)
Wealthy person - A turance yana nufin mutum mai dukiya. Misali; Maƙocinmu attajiri ne. Kishiyarta; Talaka HAU; Attajiri (Mutum mai tarin dukiya)
1 2 3 6