Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ƙam-ƙam - Tana nufin riƙe abu da ƙarfi.
Misali; Ya kamata mu riƙe addini ƙam-ƙam domin inganta rayuwarmu.
ENG; Tightly (A turance tana nufin ƙam-ƙam)
Ƙididdiga - Ƙidayawa/Ƙirgawa domin sanin haƘiƘanin yawa ko adadi na wani abu.
Ƙwadago - Dukkan wani irin aikin da mutum zai yi a biya shi kudi a matsayin lada ko albashi.
Ƙwaƙƙwafi - Bin diddigi domin gano wani ɓoyayyen al'amari.