Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kaba - Tana nufin ganyen bishiyar goruba da ake amafani da shi wajen yin tabarma da mafici da sauransu.
Misali; Tabarmar da muke zaune ta kaba ce.
ENG; Fronds of Dum-palm (A turance tana nufin kaba)
Kabari - Tana nufin ramin da ake binne mamaci.
Misali; Ya daɗe yana sana'ar haƙar kabari.
ENG; Grave (A turance tana nufin kabari)
Kabeji - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan lambu wanda ake sarrrafa shi ta hanyoyi daban-daban.
Misali; A cikin dambun akwai wadataccen kabeji.
ENG; Cabbage (A turance tana nufin kabeji)
Kabewa - Tana nufin nau'in itaciya mai ƙunshe da sinadaren da jiki ke buƙata, ana amfani da ita wajen yin miya da lemo da sauransu.
Misali; Tuwon shinkafa da miyar kabewa za a dafa.
ENG; Pumpkin (A turance tana nufin kabewa)
Kaboyi - Tana nufin hula mai faɗi da turawa suke sa wa.
Misali; Mutanen da sun kwaikwayi turawa wajen sanya hular kaboyi.
ENG; Cowboy (A turance tana nufin kaboyi)
Kaca - Tana nufin sarƙa musamman irin wadda ke juya kafar keke.
Misali; An canjawa keken kaca, yanzu yana tafiya lafiya lau.
ENG; Chain (A turance tana nufin kaca)
Kaca-kaca - Tana nufin a hargitse.
Misali; Sun yi kaca-kaca da madara a ɗakin.
ENG; Messy or disorderly (A turance tana nufin kaca-kaca)
Kacal - Tana nufin kaɗai ko kaɗan.
Misali; Naira biyar kacal za ka biya ka ɗauki kayanka.
ENG; Mere (A turance tana nufin kacal)
Kaciya - Tana nufin cire fata daga jikin al'aurar namiji.
Misali; Yara shida aka yi wa kaciya a gidan.
ENG; Circumcision (A turance tana nufin kaciya)
Kaciɓis - Tana nufin haɗuwa ba zato ba tsammani.
Misali; Mun yi kaciɓis da Gwaggo a kasuwa ɗazu.
ENG; Meeting Suddenly (A turance tana nufin kaciɓis)