Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Gaba - Tana nufin daina yi wa juna magana.
Misali; Ai sun daɗe suna gaba da juna saboda dalilin da bai kai ya kawo ba.
ENG; Enmity (A turance tana nufin gaba)
Gabani - Tana nufin lokaci da ya zo kafin wanda ake ciki.
Misali; Abin ya faru gabanin zuwan ta.
ENG; The time just before (A turance tana nufin gabani)
Gado - Tana nufin abin da ake kwanciya a kai a yi bacci ko a huta.
Misali; Ya siyo gado saboda bikin 'yarsa.
ENG; Bed (A turance tana nufin gado)
Gado - Tana nufin kuɗi da kadarorin da mamaci ke bar wa iyalansa, ma'ana duk abin da mutum ya mallaka idan ya mutu ya zama gado.
Misali; Iyalan na rikici akan rabon gado.
ENG; Inheritance (A turance tana nufin gado)
Gafaka - Tana nufin jakar fata da ake yi musamman don saka littattafai.
Misali; Malamin ya saka Al'ƙur'ani a gafaka.
ENG; Satchel (A turance tana nufin gafaka)
Gafara - Tana nufin yafiya musamman ta Allah SWT.
Misali; Allah mai gafara ne ga bayinsa.
ENG; Pardon/Forgiveness (A turance tana nufin gafara)
Gafiya - Tana nufin ƙaton ɓera.
Misali; Ramin gafiya ne a gurin.
ENG; Giant Rat (A turance tana nufin gafiya)
Gagarumi - Tana nufin babban abu mai muhimmanci.
Misali; Gwamnati ta haɗa gagarumin taron masu sana'o'in gargajiya.
ENG; Big/Important (A turance tana nufin gagarumi)
Gaggauta - Tana nufin a yi abu da sauri ko hanzari.
Misali; Ku gaggauta gamawa saboda lokacin tashi ya yi.
ENG; Hurry (A turance tana nufin gaggauta)
Gajere - Tana nufin mara tsayi.
Misali; Na rubuta gajeren labari a shafin jaridar.
ENG: Short (A turance tana nufin gajere)