Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Caca - Tana nufin wasan kati ne da ake sa kuɗi ko wani abu da zimmar wanda ya yi nasara ya ci wannan kuɗin ko abinda aka sa.
Misali; A hanyar akwai dandalin da 'yan caca suke zama.
ENG; Gambling (A turance tana nufin caca)
Cafe - Tana nufin kama abu da sauri.
Misali; Mai tsaron ragar ya cafe ƙwallon da aka bugo masa.
ENG; Catch Something (A turance tana nufin cafe)
Caje - Tana nufin duba ko ina.
Misali; Na caje yaran duka ban ga wanda ya ɗauki littafin ba.
ENG; Search (A turance tana nufin caje)
Cak - Tana nufin tsayawa ba tare da motsi ba.
Misali; Sojojin sun tsaya cak har tsawon awa ɗaya.
ENG; Stock still (A turance tana nufin Cak)
Caka - Tana nufin soka abu da ƙarfi.
Misali; Mahaucin ya caka wuƙa a jikin naman ragon.
ENG; Stab (A turance tana nufin caka)
Cakulkuli - Tana nufin taɓa kwuiɓin mutum da zimmar sa shi dariya.
Misali; Sadiya tana yi wa ƙaninita cakulkuli yana dariya.
ENG: Tickling (A turance tana nufin cakulkuli)
Cakuɗa - Tana nufin a yi ta jujjuya abu.
Misali; Amina tana cakuɗa kwaɗon zogale.
ENG; Mix Thoroughly (A turance tana nufin cakuɗa)
Cakwaikwaiwa - Tana nufin tsuntsuwa ma'abociyar rera waƙa.
Misali; Na ji cakwaikwaiwa na waƙa a kan bishiya a makarantar mu.
ENG; Sterling (A turance tana nufin cakwaikwaiwa)
Calamity - A turance yana nufin bala'i.
Misali; Ƙasashen yamma na cikin bala'i saboda afkuwar yaƙe-yaƙe.
HAU; Bala'i (Tana nufin faruwar abubuwan tashin hankali da firgici)
Cali - Tana nufin jaka mai raga-raga.
Misali; A zuba tumaturan a cikin cali saboda kar ya lalace.
ENG; Net Bag (A turance tana nufin cali)