Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Obedience - A turance tana nufin biyayya.
Misali; Aisha tana da biyayya.
HAU; Biyayya (Tana nufin yin abinda aka ce a yi da barin abinda aka hana)
Obligatory - A turance tana nufin farilla.
Misali; Yin salla sau biyar a kowacce rana farilla ne akan kowane musulmi.
HAU; Farilla (Tana nufin dole)
October - A turance yana nufin wata na goma a shekara.
Misali; Najeriya ta samu 'yanci a ranar ɗaya ga watan Oktoba 1960.
HAU; Oktoba (Wata ne na goma a shekara)
Office of the Accountant-General of the Federation - Ofishin Babban Akawun Gwamnatin Tarayya
Office of the Head of Civil Service of the Federation - Ofishin Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya
Office of the National Security Adviser - Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa Kan Tsaro
Office of the Surveyor-General of the Federation - Ofishin Shugaban Safiyo Na Gwamnatin Tarayya
Often - A turance tana nufin jefi-jefi.
Misali; Yana zuwa gaishe da kakarsa jefi-jefi.
HAU; Jefi-jefi (Tana nufin ba kodayaushe ba)
Kishiyarta; A kai-a kai
Oil Mineral Producing Areas Development Commission (OMPADEC) - Hukumar Raya Yankuna Masu Arzikin Man Fetur
Oktoba - Wata ne na goma a shekara.
Misali; Najeriya ta samu 'yanci a ranar ɗaya ga watan Oktoba 1960.
ENG; October (A turance yana nufin wata na goma a shekara)