Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Yam - A turance tana nufin doya. Misali; Doya za mu dafa yau da rana. HAU; Doya (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in abinci wanda ke sa ƙarfin jiki)
Yandagaji - Waɗanda ba kwararrun 'yanwasa ba a harkar wasanni.
Yawning - A turance tana nufin hamma. Misali; Tun ɗazu nake hamma saboda yunwa nake ji matuƙa. HAU; Hamma (Tana nufin fitar da iska ta hanyar buɗe baki wanda jin yunwa ko bacci ke sa wa)
Yelling - A turance tana nufin ihu. Misali; Matasan na ihu ne don sun ci ƙwalo. HAU: Ihu (Tana nufin ƙara ko fitar da sauti da ƙarfi)
Yuli - Wata ne na bakwai a shekara. Misali; A watan Yuli zai cika shekara biyar da gama makaranta. ENG; July (A turance yana nufin wata na bakwai a shekara)
Yuni - Wata na shida a shekara. Misali; Damina na kankama a watan Yuni. ENG; June (A turance wata ne na shida a shekara)