Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Fabrairu - Wata ne na biyu a shekara.  Misali; Za a gudanar da taron a watan Fabrairun wannan shekarar. ENG; February(A turance yana nufin wata na biyu a shekara)
Faffaɗar Jami’ar Najeriya - National Open University Of Nigeria (NOUN)
Fasaha - Azancin kirkirar wani abu mai amfani ga rayuwar dan'adam ko dabarar sarrafa tunani domin nishaɗantarwa
Fasahar Bayanai - Azancin sarrafa ko dabarar tsara bayanai
Fasahar Sadarwa - Kusan fusan fasahar bayanai ce.
Fasahar Sana’a - Dabarar sarrafa tunani wajen aiwatar da aikin ko sana'o'in hannu.
Fasting - A turance yana nufin azumi.  Misali; Ranar litinin zan yi azumi idan Allah ya kai mu. HAU; Azumi (Yana nufin barin ci da sha da mu'amalar auratayya tun daga fitowar alfijir har zuwa faɗuwar rana)
Father - A turance tana nufin mahaifi. Misali; Baba yana da jikoki arba'in a yanzu. HAU; Baba (Tana nufin mahaifi)
February - A turance yana nufin wata na biyu a shekara.  Misali; Za a gudanar da taron a watan Fabrairun wannan shekarar. HAU; Fabrairu (Wata ne na biyu a shekara)
Federal Capital Territory Administration (FCTA) - Ma'aikatar Birnin Tarayya
1 2 3 7