Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ibada - Tana nufin bautawa Allah.
Misali; Idan mutum ya kasance mai ibada rayuwarsa tana albaraka.
ENG; Serving God (A turance tana nufin ibada)
Iblis - Tana nufin sheɗan.
Misali; Allah ya raba mu da sharrin sheɗan.
ENG; Satan (A turance tana nufin sheɗan)
Iburo - Tana nufin hatsi mai kama da acca.
Misali; Na auno iburo a kasuwa.
ENG; Cereal like acca (A turance tana nufin iburo)
Icce - Tana nufin reshe ko gangar jikin bishiya da ake amfani da shi wajen hura wuta a yi girki.
Misali; Idan aka samu icce busasshe wuta tana saurin kamawa.
ENG; Wood (A turance tana nufin icce)
Idan - Tana nufin in har.
Misali; Idan an tashi daga taron za mu je ta'aziyya.
ENG; If (A turance tana nufin idan)
Idda - Tana nufin kwanakin da mace take yi bayan mijinta ya sake ta kafin ta yi wani auren.
Misali;Ta kammala idda gobe ma za a sake ɗaura mata aure.
ENG; Period during which a woman may not remarry (A turance tana nufin idda)
Idi - Tana nufin biki.
Misali; Yara na matuƙar son idi musamman na sallah babba da ƙarama.
ENG; Any major muslim festival (A turance tana nufin idi)
Ido - Tana nufin gaɓar da ake gani da ita.
Misali; Ido na ɗaya daga cikin sashen jiki mafi muhimmanci.
ENG; Eye (A turance tana nufin ido)
Idol - A turance tana nufin gunki.
Misali; Indiyawa na da gunki a gidajensu, don sun yarda shi ne abin bautarsu.
HAU; Gunki (Tana nufin sassaƙaƙƙen abu musamman wanda ake bautawa, zai iya kasancewa mai siffar mutum ko dabba da sauransu)
If - A turance tana nufin idan.
Misali; Idan an tashi daga taron za mu je ta'aziyya.
HAU; Idan (Tana nufin in har)