Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Economic Financial Crime Commission (EFCC) - Hukumar hana ta'adin tattalin arziki
Education Trust Funds (ETF) - Asusun Tallafawa llimi
Egg Shell - A turance tana nufin kamɓori. Misali; Ana haɗa hoda wacce mata ke shafawa da kamɓori. HAU; Kamɓori (Tana nufin ɓawo ko kwanson ƙwai)
Either/Or - A turance tana nufin imma. Misali; Ka zaɓi ɗaya, imma makarantar kwana ko ta je-ka-ka-dawo. HAU; Imma (Tana nufin ko)
Electric Fan - A turance tana nufin fanka. Misali; An kunna fanka a ɗakin saboda yau ana zafi. HAU: Fanka (Tana nufin na'urar da ke ba da iska)
Elephant - A turance tana nufin giwa. Misali; Giwa tana da manyan kunnuwa masu faɗi. HAU; Giwa (Tana nufin wata dabbar daji mai girma, ita ce mafi gima a cikin dabbobin da suke doron ƙasa)
Emir’s Bodyguard - A turance tana nufin dogari.  Misali; Tanimu dogari ne a masarautar Kano. HAU; Dogari (Tana nufin masu ba wa sarki tsaro)
Empty container - A turance tana nufin fanko. Misali; Gwangwanin fanko ne. HAU; Fanko (Tana nufin babu komai)
Endurance/Patience - A turance tana nufin jimiri. Misali; Duk wanda ya yi jimirin yin aiki zai samu kyakkyawan sakamako. HAU; Jimiri (Tana nufin haƙuri da juriya)
Endure - A turance tana nufin jure. Misali; Ta jure mugayen halayensa tsawon shekaru. HAU; Jure (Tana nufin dauriya)
1 2 3