Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ƙoda - Tana nufin wata muhimmiyar gaɓa da ke cikin ciki wadda ke tace jini tare da fitar da datti ta fitsari. Misali: Likita ya ce alamomin lalurarsa na kama da na ciwon ƙoda. ENG: Kidney (A turance tana nufin ƙoda)
Ƙodago - Tana nufin yin aiki domin samun kuɗi ko lada. Misali: Ya fita ƙodago domin ya sami abin tallafa wa iyalinsa. ENG: Labour / Any Work for Wages (A turance tana nufin ƙodago)
Ƙofa - Tana nufin hanyar shiga ko fita ta ɗaki, gida ko wani wuri. Misali: Ya tsaya a bakin ƙofa yana jiran a buɗe masa. ENG: Door / Doorway (A turance tana nufin ƙofa)
Ƙofi - Tana nufin haifar da tsoro ko firgici ga mutum saboda wani abu mai ban tsoro ko razanarwa. Misali: Tagwayen masu ƙofi ne shi yasa ake gudunsu. ENG: Causing fear (A turance tana nufin ƙofi)
Ƙoli - Tana nufin mafi girman daraja ko saman wani abu. Misali: Kotun ƙoli ta yanke hukunci a kan shari'ar cin hancin da ake tuhumarsu da shi. ENG: Top (A turance tana nufin ƙoli)
Ƙone - Tana nufin ƙuna ko lalacewar abu sakamakon wuta ko zafi mai yawa. Misali: Wutar ta ƙone takardun da ke kan tebur. ENG: Burn (A turance tana nufin ƙone)
Ƙorafi - Tana nufin yawan gunaguni, damuwa, ko faɗa saboda rashin jin daɗi ko rashin gamsuwa da wani abu. Misali: Yaron ya yi ta ƙorafi saboda an hana shi fita wasa. ENG: Fussing (A turance tana nufin ƙorafi)
Ƙorama - Tana nufin ƙaramin kogi ko rafin ruwa mai gudana. Misali: Mutane suna ɗebo ruwa daga ƙoramar da ke kusa da ƙauyensu. ENG: Stream (A turance tana nufin ƙorama)
Ƙosa - Tana nufin gajiya ko fusata sakamakon damuwa, wahala, ko yawan abin da ke takura mutum. Misali: Malamin ya ƙosa da hayaniyar ɗaliban aji. ENG: Become Exasperated (A turance tana nufin ƙosa)
Ƙosai - Tana nufin abincin da ake yi da markaɗaɗɗen waken da aka soya a mai. Misali: Ta yi ƙosai da safe domin karin kumallo. ENG: Bean Cakes (A turance tana nufin ƙosai)
1 333 334 335 336 337