Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Dariya - Tana nufin canja yanayin fuska tare da bayyana haƙora sakamakon wani abin farin ciki ko nishaɗi. Misali; Jama'a na ta dariya sakamakon ganin ɗan wasan barkwancin da suka yi. ENG; Laugh (A turance tana nufin dariya)  
Darkness - A turance tana nufin duhu. Misali; Gari ya yi duhu sakamakon hadarin da ya haɗo. HAU; Duhu (Tana nufin rashin haske)
Datti - Tana nufin dauɗa ko ƙazanta. Misali; Kayansa sun yi datti da yawa. ENG; Dirt (A turance tana nufin datti)
Dattijo - Tana nufin babban mutum mai kima wanda shekarunsa suka ja. Misali; Mahaifinta dattijo ne saboda yana da dattako. ENG; An elder (A turance tana nufin dattijo)
Daula - Tana nufin dukiya ko kayan alatu da ƙawa na duniya. Misali; Lami tana cikin daula saboda mijinta yana da kuɗi. ENG; Wealth (A turance tana nufin daula)
Dauriya - Tana nufin juriya. Misali; Tanko yana da dauriya. ENG: Ability to endure hardship or pain (A turance tana nufin dauriya)
Daushe - Tana nufin tsohon goro. Misali; Gwaggo ta fi son goro daushe. ENG; Last year's kolanuts (A turance tana nufin daushe)
Dawa - Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in hatsi. Misali; Tuwon dawa na ƙara lafiya saboda tana ƙunshe da sinadarai masu inganta lafiya. ENG: Guinea Corn (A turance tana nufin dawa)
Dawo - Tana nufin fura ba tare da nono ba. Misali; Sakkwatawa na son dawo, sukan sha shi kodayaushe. ENG; Ball of fura without milk (A turance tana nufin dawo)
Day After Tomorrow - A turance tana nufin jibi. Misali; Jibi za a fara bikin kuma sai an jera sati ana yi. HAU; Jibi (Tana nufin ranar da ke bin gobe)
1 84 85 86 87 88 337