Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Debt Management Office (DMO) - Ofishin harkokin bashi
December - A turance yana nufin wata na ƙarshe a shekara.
Misali; Watan Disamba yana da kwana talatin da ɗaya.
HAU; Dismba (Wata ne na ƙarshe a shekara)
Decide - A turance tana nufin ƙudura.
Misali: Ya ƙudura a ransa cewa zai ci gaba da karatunsa duk da tarin ƙalubalen da yake fuskanta.
HAU: Ƙudura (Tana nufin yanke shawara da cimma matsayar yin wani abu bayan an yi tunani)
Defense Intelligence Agency (DLA) - Hukumar leƙen asiri ta soji
Delay - A turance tana nufin jinkiri.
Misali; An samu jinkiri wajen fitar da sakamakon jarrabawar saboda wasu ƙwararan dalilai.
HAU; Jinkiri (Tana nufin dakatawa ko ɗaukan lokaci)
Deleb Palm - A turance tana nufin giginya.
Misali; Gingiya tana da zaƙi da kuma maganin basir.
HAU; Giginya (Tana nufin ɗaya daga cikin 'ya'yan itaciya masu amfani ga ɗan Adam, kama daga ƙwallonta da ganyenta da ma ita kanta)
Democracy - A turance tana nufin gwamnatin da aka kafa ta hanyar zaɓe.
Misali; A Najeriya mulkin damokuraɗiyya ake yi.
HAU; Damokuraɗiyya (Tana nufin gwamnatin da jama'a suka kafa ta hanyar zaɓe)
Dense Crowd - A turance tana nufin cincirindo.
Misali; Mutane sun yi cincirindo a ƙofar gidan sarki.
HAU; Cincirindo (Tana nufin taruwar mutane da yawa)
Deny - A turance tana nufin ƙaryata.
Misali; An zarge shi da laifi amma ya ƙaryata hakan.
HAU; Ƙaryata (Tana nufin ƙin amincewa da wani abu ko musanta shi)
Department - Sashe, Ma'aikata