Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Dull - A turance tana nufin daƙiƙi. Misali; Sun ce masa daƙiƙi saboda ya faɗi jarrabawa. HAU; Daƙiƙi (Tana nufin wanda ba ya gane karatu)
Dung beetle - A turance tana nufin buzuzu. Misali; Buzuzu ya fito a ƙofar gidan shi yasa ba zan iya shiga ba. HAU; Buzuzu (Tana nufin wani nau'in ƙwaro mai tashi)    
Dutse - Tana nufin dunƙulallun halittun Allah da ke doron ƙasa. Misali; Akwai gungumemen dutse a garin mu. ENG; Stone (A turance tana nufin dutse)
Dye-pit - A turance tana nufin karofi. Misali; Na taɓa ganin karofi a marinar da ke unguwar Ƙofar Mata. HAU; Karofi (Tana nufin rami mai ɗauke da ruwan da ake rina tufafi)
Dysentary - A turance yana nufin atini. Misali; Yara kan yi atini sakamakon shan zaƙi da suke yi. HAU; Atini (Yana nufin ba-haya mai danƙo kuma mai wahalar fita wanda shan zaƙi ke haddasawa)
Ear - A turance tana nufin kunne. Misali; Yara na yawan yin ciwon kunne musamman lokacin sanyi. HAU; Kunne (Tana nufin gaɓar da ake ji da ita)
Economic Financial Crime Commission (EFCC) - Hukumar hana ta'adin tattalin arziki
Eczema - A turance tana nufin kirci.  Misali; Abin da yasa almajirai suke yin kirci shi ne rashin wanka. HAU; Kirci (Tana nufin wasu ƙuraje masu matuƙar ƙaiƙayi da ke fitowa a fata sakamakon rashin tsabta)
Education Trust Funds (ETF) - Asusun Tallafawa llimi
Egg Shell - A turance tana nufin kamɓori. Misali; Ana haɗa hoda wacce mata ke shafawa da kamɓori. HAU; Kamɓori (Tana nufin ɓawo ko kwanson ƙwai)
1 87 88 89 90 91 300