Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Envy - A turance tana nufin hassada.
Misali; Daga cikin munanan ɗabi'u akwai hassada da kuma ƙarya.
HAU; Hassada (Tana nufin jin ƙyashi ko baƙin ciki idan wani ya samu abin alkhairi ko cigaba ko ɗaukaka da sauransu)
Epilepsy - A turance tana nufin farfaɗiya.
Misali; An buɗe asibitin masu farfaɗiya a garin da muke.
HAU; Farfaɗiya (Tana nufin lalurar da ta shafi ƙwaƙwalwa, wadda ke sa mutum ya fita hayyacinsa ya faɗi yana shure-shure)
European - A turance tana nufin bature.
Misali; Mr. Mike baturen Ingila ne.
HAU; Bature (Tana nufin mutum farar fata wanda ya zo daga Turai)
Every Day - A turance tana nufin kullum.
Misali; Mukan yi salla sau biyar a kullum.
HAU; Kullum (Tana nufin kowacce rana)
Everyone - A turance tana nufin kowa.
Misali; Kowa zai iya neman tallafin da gwamnati take bayarwa.
HAU; Kowa (Tana nufin mutane baki ɗaya)
Examination - A turance tana nufin jarrabawa.
Misali; Suna gama jarrabawa za a ba su hutu.
HAU; Jarrabawa (Tana nufin gwaji)
Except - A turance tana nufin face.
Misali; Babu wanda zai makara face ya kasance mai saɓa alƙawari.
HAU; Face (Tana nufin sai dai)
Excessive Desire - A turance tana nufin jaraba.
Misali; Shan giya ya zama jaraba gare shi, sai ya sha yake jin daɗi.
HAU; Jaraba (Tana nufin jin so mai tsanani)
Excessive Fat - A turance tana nufin ɓulɓul.
Misali; Jamila ta yi ɓulɓul tunda ta dawo daga Ikko.
HAU; Ɓulɓul (Tana nufin ƙiba sosai)
Executioner - A turance tana nufin hauni.
Misali; Ɓarayin sun gamu da hauni a kotu.
HAU; Hauni (Tana nufin mai yanke hukuncin kisa)