Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Explain Thoroughly - A turance tana nufin fayyace.
Misali; Malamin ya fayyace mana darasin dalla-dalla.
HAU; Fayyace (Tana nufin yin cikakken bayani)
Explanation - A turance yana nufin bayani.
Misali; Malami yana yi wa ɗalibai bayani akan darasin larabci.
HAU; Bayani (Tana nufin yin magana don fahimtarwa)
Extreme Degree - A turance tana nufin innanaha.
Misali; Ai munafiki ne na innanaha.
HAU; Innanaha (Tana nufin ƙololuwa)
Extreme End - A turance tana nufin gaya.
Misali; Yaran sun yi ƙoƙari matuƙa gaya.
HAU; Gaya (Tana nufin ƙololuwa ko ƙarshe)
Eye - A turance tana nufin ido.
Misali; Ido na ɗaya daga cikin sashen jiki mafi muhimmanci.
HAU; Ido (Tana nufin gaɓar da ake gani da ita)
Eyebrow - A turance tana nufin gira.
Misali; Haramun ne aske gashin gira a musulunci.
HAU; Gira(Tana nufin gurbin da ke tsakanin ido da goshi, yana ɗauke da gashi amma ba mai yawa ba)
Fa’ida - Tana nufin amfanin abu.
Misali; Zumunci yana da fa'ida don yana sa albarka a rayuwa.
ENG; Usefulness (A turance tana nufin fa'ida)
Kishiyarta; Rashin Fa'ida
Fabrairu - Wata ne na biyu a shekara.
Misali; Za a gudanar da taron a watan Fabrairun wannan shekarar.
ENG; February(A turance yana nufin wata na biyu a shekara)
Facaka - Tana nufin kashe kuɗi ba tare da la'akari ba.
Misali; Tun da aka raba musu gado yake facaka da kuɗi.
ENG; Squandering (A turance tana nufin facaka)
Face - Tana nufin sai dai.
Misali; Babu wanda zai makara face ya kasance mai saɓa alƙawari.
ENG; Except (A turance tana nufin face)