Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Face - A turance tana nufin fuska.
Misali; Ta mare shi a fuska hakan ya janyo suka fara faɗa.
HAU; Fuska (Tana nufin sashen jiki mai ƙunshe da ido da hanci da baki)
Faci - Tana nufin sacewar taya.
Misali; Tayar keken ta yi faci sai an an gyaro.
ENG; Patch (A turance tana nufin faci)
Facial Markings - A turance tana nufin jarfa.
Misali; Jarfa, gadon gidansu ne.
HAU; Jarfa (Tana nufin tsagun fuska)
Fade - A turance tana nufin koɗe.
Misali; Atamfar ta koɗe saboda ta sha wanki a kai a kai.
HAU; Koɗe (Tana nufin canja yanayi ko launi musamman sakamakon jin jiki)
Faffaɗar Jami’ar Najeriya - National Open University Of Nigeria (NOUN)
Fage - Tana nufin fili ko dandali.
Misali; An ba wa 'yan dambe fage don su fafata.
ENG; Open Space/Arena (A turance tana nufin fage)
Fahimta - Tana nufin ganewa.
Misali; Ɗaliban suna da fahimta ƙwarai da gaske.
ENG; Understand (A turance tana nufin fahimta)
Kishiyarta; Rashin Fahimta
Fail To Do - A turance tana nufin gaza.
Misali; Sakamakon da ya samu ya gaza kai wa yanda za a ɗuake shi a jami'a.
HAU; Gaza (Tana nufin kasawa)
Failure - A turance tana nufin kuskure.
Misali; Idan mutum ya yi kuskure ya kamata a yi masa afuwa.
HAU; Kuskure (Tana nufin yin abu ba daidai ba)
Faith - A turance tana nufin imani.
Misali; Yarda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau na ɗaya daga cikin rukunan imani.
HAU; Imani (Tana nufin yarda, amincewa ko ba da amanna ɗari bisa ɗari)