Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Fake - Tana nufin samun mafaka. Misali; Lokacin da ruwan ya sakko a shagon na fake. ENG; Take shelter or refuge (A turance tana nufin fake)
Fake - A turance tana nufin jabu. Misali; Madarar jabu ce, idan aka sha tana sa ciwon ciki. HAU; Jabu (Tana nufin abin da ba shi da inganci)
Fako - Tana nufin ɓuya don kai harin ba-zata. Misali; Shi suke fako, yana zuwa suka cafke shi. ENG: Ambush (A turance tana nufin fako)
Faku - Tana nufin mutuwar annabawa ko bayin Allah salihai. Misali; Ba su san annabi ya faku ba. ENG; Death (of prophets or saints) (A turance tana nufin faku)
Falala - Tana nufin alkhairai da dama. Misali; Akwai ɗimbin falala a cikin ambaton Allah. ENG; Abundance, Fortune (A turance tana nufin falala)
Fale-Fale - Tana nufin abu mara nauyi ko kauri. Misali; Yadin da aka ba mu fale-fale ne ba shi da kauri. ENG; Thin and Flimsy (A turance tana nufin fale-fale)
Fallasa - Tana nufin tona asiri. Misali; An fallasa abin da suka daɗe suna ƙullawa yau. ENG;Disclose Secret (A turance tana nufin fallasa)
Falmaran - Tana nufin riga mara hannu da ake ɗorawa a kan mai dogon hannu. Misali; Falmaran ɗin da yarima ya sa ta yi kyau ƙwarai da gaske. ENG;Waistcoat (A turance tana nufin falmaran)
Famfara - Tana nufin cirewar da haƙoran yara ke yi kafin na girma ya fito. Misali; Muntari yana famfara. ENG; Losing Baby Teeth (A turance tana nufin famfara)
Family - A turance tana nufin iyali. Misali; Yana kula da iyali yanda ya kamata. HAU; Iyali (Tana nufin ahali ko kuma uwa da uba da yaransu)
1 92 93 94 95 96 300