Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Dutse - Tana nufin dunƙulallun halittun Allah da ke doron ƙasa. Misali; Akwai gungumemen dutse a garin mu. ENG; Stone (A turance tana nufin dutse)
Dye-pit - A turance tana nufin karofi. Misali; Na taɓa ganin karofi a marinar da ke unguwar Ƙofar Mata. HAU; Karofi (Tana nufin rami mai ɗauke da ruwan da ake rina tufafi)
Dysentary - A turance yana nufin atini. Misali; Yara kan yi atini sakamakon shan zaƙi da suke yi. HAU; Atini (Yana nufin ba-haya mai danƙo kuma mai wahalar fita wanda shan zaƙi ke haddasawa)
Ear - A turance tana nufin kunne. Misali; Yara na yawan yin ciwon kunne musamman lokacin sanyi. HAU; Kunne (Tana nufin gaɓar da ake ji da ita)
Earth - A turance tana nufin ƙasa. Misali; Allah ya yi halittu masu yawa a doron ƙasa. HAU; Ƙasa (Tana nufin duniyar da muke rayuwa a kanta)
Economic Financial Crime Commission (EFCC) - Hukumar hana ta'adin tattalin arziki
Eczema - A turance tana nufin kirci.  Misali; Abin da yasa almajirai suke yin kirci shi ne rashin wanka. HAU; Kirci (Tana nufin wasu ƙuraje masu matuƙar ƙaiƙayi da ke fitowa a fata sakamakon rashin tsabta)
Education Trust Funds (ETF) - Asusun Tallafawa llimi
Effort - A turance tana nufin ƙoƙari. Misali: Ƙoƙarinsa wajen karatu ya sa ya yi nasara a jarabawa. HAU: Ƙoƙari (Tana nufin ƙwazo ko amfani da ƙarfi da himma domin cimma wani buri ko nasara)
Egg Shell - A turance tana nufin kamɓori. Misali; Ana haɗa hoda wacce mata ke shafawa da kamɓori. HAU; Kamɓori (Tana nufin ɓawo ko kwanson ƙwai)
1 94 95 96 97 98 337