Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Fartanya - Tana nufin wani ƙarfe mai ƙota da ake amfani da shi don yin noma.
Misali; Ado ya saɓa fartanya ya nufi gona.
ENG; Hoe (A turance tana nufin fartanya)
Fasaha - Azancin kirkirar wani abu mai amfani ga rayuwar dan'adam ko dabarar sarrafa tunani domin nishaɗantarwa
Fasahar Bayanai - Azancin sarrafa ko dabarar tsara bayanai
Fasahar Sadarwa - Kusan fusan fasahar bayanai ce.
Fasahar Sana’a - Dabarar sarrafa tunani wajen aiwatar da aikin ko sana'o'in hannu.
Fassara - Tana nufin daga wani harshe zuwa wani harshe.
Misali; Ya fassara littafin daga harshen larabci zuwa harshen Hausa.
ENG; Translation (A turance tana nufin fassara)
Fasting - A turance yana nufin azumi.
Misali; Ranar litinin zan yi azumi idan Allah ya kai mu.
HAU; Azumi (Yana nufin barin ci da sha da mu'amalar auratayya tun daga fitowar alfijir har zuwa faɗuwar rana)
Fasto - Tana nufin limamin coci.
Misali; Maƙococinsa babban fasto ne.
ENG; Pastor (A turance tana nufin fasto)
Fat - A turance tana nufin ɓulele.
Misali; Sabon ɗalibin da aka kawo mana ɓulele ne.
HAU; Ɓulele (Tana nufin mai ƙiba)
Fat On Meat - A turance tana nufin kitse.
Misali; Ragon yana da kitse ainun, maiƙon jikinsa ya isa a soya shi.
HAU; Kitse (Tana nufin maiƙon da ke jikin nama)