Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Faɗa - Tana nufin ɗaga murya da faɗin maganaganu marasa daɗi saboda ɓacin rai. Misali; Ɗaliban faɗa suke bayan an tashi daga makaranta. ENG; Quarrel (A turance tana nufin faɗa)
Faƙiri - Tana nufin talaka wanda ba shi da komai. Misali; Idan za ka yi sadaka ka nemi faƙiri ka ba shi. ENG; Poor, Destitute (A turance tana nufin faƙiri)
February - A turance yana nufin wata na biyu a shekara.  Misali; Za a gudanar da taron a watan Fabrairun wannan shekarar. HAU; Fabrairu (Wata ne na biyu a shekara)
Feda - Tana nufin inda ake sa ƙafa a tuƙa keke. Misali; Keken na da matsalar feda sai an gyara. ENG; Bicycle Pedal (A turance tana nufin feda)
Federal Capital Territory Administration (FCTA) - Ma'aikatar Birnin Tarayya
Federal Character Commission (FCC) - Hukumar  Raba-Daidai Ta kasa
Federal Civil Service Commission (FCSC) - Hukumar ma'aikatan Gwamnatin Tarayya
Federal Environmental Protection Agency (FEPA) - Hukumar kare mahalli Ta kasa
Federal Executive Council (FEC) - Majalisar Zartarwa Ta Ƙasa
Federal High Court - Babbar Kotun Ƙasa
1 97 98 99 100 101 300