Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Famous - A turance tana nufin fitacce.
Misali; Alh. Sule fitacce ne a unguwar.
HAU; Fitacce (Tana nufin wanda ya shahara)
Fanka - Tana nufin na'urar da ke ba da iska.
Misali; An kunna fanka a ɗakin saboda yau ana zafi.
ENG: Electric Fan (A turance tana nufin fanka)
Fanke - Tana nufin nau'in abin ci da ake yi da fulawa da sikari da mai da sauransu.
Misali; An yi sadakar fanke a gidan mutuwar.
ENG; Fried cake made of wheat flour (A turance tana nufin fanke)
Fanko - Tana nufin babu komai.
Misali; Gwangwanin fanko ne.
ENG; Empty container (A turance tana nufin fanko)
Fansho - Tana nufin kuɗin da ake ba wa mutum bayan ya kammala shekarun aikinsa.
Misali; Ma'aikata da dama da fansho suke siyan gida.
ENG; Pension (A turance tana nufin fansho)
Faraga - Tana nufin samun dama.
Misali; Mun samu faraga mun yi abubuwan alkhairi da yawa.
ENG; Opportunity (A turance tana nufin faraga)
Faranta - Tana nufin sanya farin ciki.
Misali; Matar ta faranta ran mijinta ta hanyar yi masa girki.
ENG; Gladden (A turance tana nufin faranta)
Faranti - Tana nufin mazubin abinci.
Misali; Ki zuba abincin a faranti don ya huce da wuri.
ENG; Plate (A turance tana nufin faranti)
Farar-Hula - Tana nufin wanda ba soja ko mai ɗamara ba.
Misali; A Najeriya mulkin farar-hula ake yi.
ENG; Civilian (A turance tana nufin farar-hula)
Kishiyarta; Soja
Farashi - Tana nufin kuɗin abu.
Misali; Ana ta ƙarawa kaya farashi a kasuwa saboda karyewar tattalin arziƙi.
ENG; Price (A turance tana nufin farashi)