Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Damtse - Tana nufin gaɓar da take saman hannu. Misali; Masu manyan damtse yawancin su ƙarfafa ne. ENG; Fore-arm (A turance tana nufin damtse)
Dandali - Tana nufin filin da samari da 'yan mata ke taruwa a ƙauyuka da birane don yin wasanni da nishaɗi. Misali; 'Yan mata na rawa a dandali. ENG; Central open space in village or town (A turance tana nufin dandali)
Dandalin Wasan Kwaikwayo Na Ƙasa - National Theater
Dandamali - Tana nufin ɗan tudu da ake yi kofar ɗaki. Misali; Inna tana zaune a kan dandamali. ENG; Raised Doorstep (A turance tana nufin dandali)
Dandaƙa - Tana nufin daka abu har ya zama gari. Misali; Za mu dandaƙa geron kafin mu yi kunu da shi. ENG: Pound and Crush something (A turance tana nufin dandaƙa)
Dandi - Tana nufin yawo da rayuwa ta rashin mafaɗi. Misali; Ta dawo daga yawon dandi ɗauke da cuta mai tsanani. ENG: Roaming about leading a loose, carefree life (A turance tana nufin dandi)
Dandruff -

A turance tana nufin kwarkwashi.

Misali: Ta sayi maganin kwarkwashi domin rage yawan lalacewar da gashin kanta ke yi.

HAU; Kwarkwashi (Tana nufin farin ɓawon da ke fitowa a matsirar gashin kai wanda ke lalata gashi da karairaya shi)

Dandruff -  A turance yana nufin farin abu da yake fitowa ta matsirar gashin kai. Misali; Indo tana da amosani sosai a kanta. HAU; Amosani (Wani farin abu ne da yake fitowa ta matsirar gashin kai, mai sa ƙaiƙayi da kuma lalacewar gashi.)
Danga - Tana nufin kewaye gida da karan masara. Misali; Baba yana waje jikin danga tare da amininsa suna magana. ENG; Cornstalk Fence (A turance tana nufin danga)
Dangantaka - Tana nufin alaƙa.  Misali;Akwai dangantaka tsakanin angon da amaryar. ENG; Relationship (A turance tana nufin dangantaka)
1 82 83 84 85 86 337