Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Dakali - Tana nufin gini mai ɗan tudu da ake yi a ƙofar gida don zama. Misali; Baba yana zaune a kan dakali da abokinsa suna hira. ENG; Low mud platform outside compound (A turance tana nufin dakali)
Dakaru - Jam'in dakare, jarumai masu tafiya yaki a kafa, kamar sojan kasa a yanzu.
Dakau - Tana nufin yin daka a matsayin sana'a. Misali; Matar Ado dakau take yi a unguwarsu. ENG: Pounding corn for pay (A turance tana nufin dakau)
Dakile - Hanawa, kamar hana wani al'amari musamman mara kyau ko barna cigaba da faruwa ko yaduwa
Dako - Tana nufin ɗaukarwa mutum kaya a kai masa inda yake so, ya biya. Misali; Ƙungiyar masu dako sun koka kan ƙarancin biyansu da mutane ke yi. ENG; Carrying load for payment (A turance tana nufin dako)
Dakushe - Tana nufin rashin kaifi. Misali; Wuƙaƙen sun dakushe sai an wasa su. ENG; Blunt (A turance tana nufin dakushe)
Dala - Tana nufin nau'in kuɗin ƙasar Amurka. Misali; Babu Nera a lalitarsa sai Dala. ENG; Dollar (A turance tana nufin dala)
Dalala - Tana nufin zubar yawu daga baki ba ƙaƙƙautawa. Misali; Yawu yana dalala daga bakinsa saboda nauyin bacci. ENG;Dribble (of saliva) (A turance tana nufin dalala)
Dalla-Dalla - Tana nufin yin abu daki-daki a bayyane. Misali; Malamin yana bayani dalla-dalla ga ɗalibansa. ENG; Clearly (A turance tana nufin dalla-dalla)
Damage - A turance tana nufin ɓarna. Misali; An yi iska mai ƙarfi jiya kuma ta yi ɓarna sosai HAU; Ɓarna (Tana nufin lalata abu)
1 80 81 82 83 84 337