Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Black-hooded Cobra - A trurance tana nufin kumurci. Misali; Kumurci ya sari kaka a gona. HAU; Kumurci (Tana nufin baƙin maciji mai dafi)
Black-hooded Cobra - A turance tana nufin gamsheƙa. Misali; Mun ga gamsheƙa a hanyar gonar Malam Mudi. HAU: Gamsheƙa (Tana nufin ƙaton baƙin maciji)
Blackboard - A turance yana nufin allon rubutu. Misali; Malami yana rubutu a kan allo. HAU; Allo (Abin rubutu ne galibi na katako)
Blanket - A turance tana nufin bargo. Misali; Indo ta wanke bargon da ta siyo ran Asabar. HAU; Bargo (Tana nufin abin lulluɓa don jin ɗumi da kuma kariya daga jin sanyi)
Blinking - A turance tana nufin ƙifce. Misali: Jaririyar tana ƙifce ido saboda hasken rana ya yi mata ƙarfi. HAU: Ƙifce (Tana nufin rufe ido da buɗe shi cikin sauri, musamman saboda haske ko motsi)
Blood - A turance tana nufin jini. Misali; Likita ya ce sai an ƙara masa jini leda ɗaya. HAU; Blood (Tana nufin sinadarin ruwa mai launin ja wanda zuciya take harbawa sassan jiki, yana ƙunshe da abubuwan da jiki ke buƙata domin rayuwa)
Blow - A turance tana nufin hura. Misali; Tun ɗazu nake hura wutar ta ƙi kamawa. HAU; Hura (Tana nufin fito da iska ta baki)
Blow One’s Nose - A turance tana nufin fyace. Misali; Tun ɗazu take fyace hanci saboda mura ta kama ta sosai. HAU; Fyace (Tana nufin fitar da majina daga hanci da ƙarfi)
Blunt - A turance tana nufin dakushe. Misali; Wuƙaƙen sun dakushe sai an wasa su. HAU; Dakushe (Tana nufin rashin kaifi)
Boasting - A turance tana nufin kuri. Misali; Safiyanu ya cika kuri, amma ana taɓa shi zai fara kuka. HAU; Kuri (Tana nufin cika baki ko kambama kai)
1 33 34 35 36 37 337