Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Biskit - Tana nufin abin ci na maramari da ake yi da fulawa da sikari da wasu sinadaran. Misali; Biskit ɗin kamfanin NASCO yana da daɗi da inganci. ENG; Biscuit (A turance yana nufin biskit)
Bita - Tana nufin nanata karatu. Misali; Ɗalibai na bita a cikin aji tun safe. ENG; Reading again through a text (A turance tana nufin bita)
Bitch - A turance tana nufin karya. Misali; Wata karya ce ta haihu a bayan layinmu. HAU; Karya (Tana nufin macen kare)
Bitterness - A turance tana nufin ɗaci. Misali; Maganin yana da ɗaci sosai. HAU; Ɗaci (Tana nufin wani yanayi mara daɗi da ake ji a maƙogwaro idan an ɗanɗana abubuwa kamar magani da sauransu)
Biya - Tana nufin bayar da kuɗi sakamakon wani aiki, ko bayar da wani abu a dalilin yin wani aiki. Misali; An biya ma'aikata albashin su na wannan watan. ENG; Pay (A turance tana nufin biya)
Biyayya - Tana nufin yin abinda aka ce a yi da barin abinda aka hana. Misali; Aisha tana da biyayya. ENG; Obedience (A turance tana nufin biyayya)
Biɗa - Tana nufin nema ko lalube. Misali; Ya samu abinda ya je biɗa a balaguron da ya yi. ENG; Search (A turance yana nufin biɗa)
Biƙi - Tana nufin wankan jego da mace take yi daga ranar da ta haihu zuwa kwana arba'in. Misali; Yayata biƙi take yi, yau kwana huɗu. ENG; Hot bath taken by women after delivery (A turance tana nufin biƙi)
Blabbing -

A turance tana nufin kwarmato.

Misali: An hana shi shiga taro saboda halinsa na kwarmato.

HAU; Kwarmato (Tana nufin yawan faɗin sirri ko magana ba tare da ɓoye abu ba)

Black - A turance tana nufin baƙi. Misali; Ina neman baƙin takalmi zan siya. HAU; Baƙi (Tana nufin launi mai duhu)
1 32 33 34 35 36 337